Friday, July 29, 2011

KARIN AURE

Assalamu alaikum. A gurguje ina sanar da masu karatuna cewar Allah Ya azurta ni da karin aure ranar 16 ga Yuli 2011. Aurena na farko na yi shine ranar 6 ga Disamba 1998.
Na san akwai masu tambayar dalilin da yasa zan kara mata, menene dalili da sauransu to amma kasancewata Musulmi, Bahaushe ina ganin tsayawa nayi bayani kamar bata baki ne. A kullum abu ya samu mutum to mu kan danganta shi da kaddara duk da wasu zasu ce ai tilas sai mutum ya tanka. Haka ne.
Amma da farko a takaice dai ina zaton an fara maganar aure ne daga biyu ba daya ba. To ni ba malami ba ne, abin kawai da na sani shine Allah Ya bani kyauta kuma ina ganin ban isa na ce bana so ba. Ina matukar kaunar matata ta farko to amma tasowarmu a iyali da suka kasance mata a hade ban samu matsala ta azo a gani ba. Haka ina matukar kaunar amarya ta wacce ta nuna min kauna fiye da wata 'ya, kuma nayi kokarin ganin saka mata da abinda take kauna.
A duk lokacin da akayi karin aure addu'ar ita ce Allah Ya bada zama lafiya, Ya hada kansu, shi kuma mijin Allah Ya bashi ikon yin adalci. Don haka nake rokon addu'a daga kowa da kowa.
Na gode.

Wednesday, March 30, 2011

Sharhin Fim din Halak Malak

SHARHIN FIM DIN HALAK MALAK
Yusuf Ubale Ajingi
(www.yusufubale.blogspot.com, e-mail: yusufaubale@yahoo.com)

Masu Fadakarwa:
TY Shaban, Saratu Gidado, Samira Ahmad, Muhd S. Bashir, Lawan M. Adam, Umar Gombe, Badiya Ibrahim.

Labari: Rahama Y. Shaban
Kula da Shiri: Abba Kuta
Dandali: Ibrahim Ross
Ci gaban Shiri: Lawan M. Adam
Shawara: Muhammad Sango
Daukar Hoto: Hashimu Dikku, Asmancy, Sani Hikima
Tsara Hoto: Sulaiman Abubakar, Nura Abubakar
Daukar Nauyi: Effect Crew Family da Safjamil studioz
Shiryawa: TY Shaban
Umarni: I.M.A. El-Muazzam

Gabatarwa
'... Amma ni labarin 'Halak Malak' ban dauki wannan bangaren ba, sai ya zamana ita yarinyar bata zamo jigo ko gishirin labarin ba, don haka nake ganin ni dai ban taba ganin irin wannan labarin ba a finafinan Hausa ba, domin labari ne wanda ana zaton wuta a makera, sai gata a masaka'. Wannan itace maganar da mai shiryawa TY Shaban yayi a Mujallar fim, ta Janairu 2011 kan fim din Halak Malak.

Jigo
Ana zaton wuta a makera, sai gata a masaka.

Labari
Fim din ya fara ne da haduwar Hassan (Shaban TY) da wata yarinya Fatima (Samira Ahmed) a lokacin suna tare da abokinsa Jafar (Lawan M. Adam) inda yayi shawa’ar aurenta. Kuma akayi auren bayan wata daya.

To amma Hassan yafi dan’uwansa Hussaini (Shaban TY) hankali musamman yadda ake nuna yadda suke zaune da mahaifiyarsu Saratu Gidado. Sannan ga shi shi Hassan shi yake tafiyar da kasuwancin da mahaifinsu ya rasu ya bari. Duk da samun riba ta fiye da Naira Miliyan hamsin amma Hassan ya nemi Hajiya ta saka baki domin Hussaini ya sanya hannu kan takardar da zata bashi damar daukar kudi domin shiga harkokin kasuwanci na kasashen waje wadda wani abokinsa Zaki (Muhd S. Bashir) ya kwadaita masa. Shi dai Hussaini ya dage kan dalilinsa na cewar akwai hadari a cikin kasuwancin kuma tun da na magada ne to kawai a bashi iya nasa ya je yayi.

A bangare daya Hussaini yana da wata budurwa Dija (Badiya Ibrahim) wacce suke matukar kaunar juna. Shi kuma Hassan bayan jan hankalinsa da abokinsa yayi masa ya yi zurfi wajen damuwa kan yadda zai samu yarjewar dan’uwansa.

Hussaini ya nemi fita shakatawa da budurwar tasa wacce ta yi matukar mamaki da nuna rashin yardar. A haka har dai ya samu nasarar aika-aika da ita wadda a karshe ta samu juna biyu. A sakamakon haka ta je wurin Hassan ta kai karar Hussaini shi kuma yace zai dau mataki. Ta kuma kai wa Hussaini takardar gwajin ciki da aka yi mata, shi kuma mamaki ya rufe shi da kin yarda.

Hassan ya kira shi ya bayyana masa cewar ya san duk abinda ya aikata don haka idan baya son tonan asiri to ya sa hannu a takardar. Tilas Hussaini ya saka hannu ta yarda a debi kudin.

Zaki dai ya samu nasarar karbar cekin kudin kuma har ya fita harkokin kasuwancinsa.

Ita kuma Hajiya ta kara tabbatarwa cewar Hussaini ba mutumin kirki ba ne tun da gashi har yayiwa wata ciki ga kuma kin sa hannu kan takardar da dan uwansa zai yi amfani da kudi.

Zaki dai ya turowa da Hassan cewar kudi sun shiga ma’ajiyarsa ta banki don haka yana China kuma sun ishe shi yin kasuwanci, don haka yana yi masa ban kwana. Nan take ciwon zuciya ya kama Hassan bisa wannan abin bakin ciki. Anan Hajiya ta tabbatar da gaskiyar Hussaini na kin amincewa da shi yayi amfani da kudin, shi kuma Hussaini gashi yayi aika-aika ta yiwa wata ciki. Anan dai Allah Ya karbi ran Hassan.

Abokin su watau Jafar yayi da-na-sanin abubuwan da suka faru kuma nan ya je wurin Hajiya yana bayyana mata duk abubuwan da suka faru musamman yadda Hassan ya bayyana masa matsalar ko zai taimaka masa domin shawo kan Hussaini ya sa hannu kan takardar, shi kuma Jafar ya fada masa cewar ya kamata ya je wurin Dija yayi shiga irin ta Hussaini domin rudarta don salkayo shi ya yarda. Wanna shiri shine ya sa har ya janyo yayi wa Dija ciki ita kuma tayi zaton Hussaini ne. Hajiya tayi kokwanton wannan zance na Jafar amma ya nuna shaidar agogo mai tsada da Hassan ya bashi a matsayin tukwucin aikinsa. Nan Hajiya ta tabbatar da maganar bahaushe ta ana zaton wuta a makera sai gata a masaka. Nan ta sa Jafar ya nemo mata Hussaini wadda ta kora daga gidan. Ya dai dawo da shi wadda bayan wata uku Hajiya ta nemi Fatima ta yarda ta auri Hussaini tun da Musulunci ya yarda da mace ta aurin kani idan yaya ya rasu, kuma ta mallaka masa ita halak malak.
Hussaini ya ci gaba da harkokin kasuwancin da Hassan ya bari inda har Nasir (Umar Gombe) ke taya shi murnar samun ci gaba da kuma yafe duk wasu kudade da yake bi.

A karshe dai Fatima ta samu juna biyu da Hussaini.


Sharhi
Fim din ya burge musamman saboda wadannan dalilan:
• Jigon sa ba wai soyayya bace kuma ba yarinyar ce karfin labarin ba.
• Fim din ya ginu ne kan cin amana, yin amfani da sunan wani don cimma wata manufa da kuma fassara hukumcin auren mace ga dan’uwan mijin bayan rasuwarsa wadda abin burgewa ne musamman saboda wadannan abubuwa yanzu suna faruwa a cikin al’umma.
• Labarin fim din a bayyane yake ta yadda mai kallo zai fahimci matakai dabam-daban ba tare da hargitsa shi ba; Fim ne mai saukin ganewa da kuma isar da sako kai tsaye.
• An yi kokari wajen jan hankalin mai kallo ta yadda bai taba zaton cewar Hassan ne yayi shiga irin ta Hussaini yayi wa Dija ciki ba.
• Ana zaton Hussaini yadda yake wajen huldataiya haka a kowacce harka yake a sauran abubuwan don haka mai kallo zai zaci cewar Hassan ya fi shi gaskiya ashe ba haka ba ne.
• Rashin sanya waka sai a karshen fim din a wurin da ta dace ya burge.
• Duk kan masu fadakarwa sun burge, kayan sanyawa, gida, ofis sun dace.
• Amfani da mashawarci yana kara fito da finafinan Hausa.Gyare-gyare
1. Yin amfani da mota guda daya ga Hassan a lokacin da zai yi shigar sojan gona wajen budurwar dan’uwansa da kuma lokacin da Zaki yake zuwa wajensa da ita duk da ba’a nuna har kusancinsa da shi ba ya kai suna musanyar mota ba bai dace ba.
2. Yadda aka bata lokaci wajen nuna motar da yadda take rufe kanta (conversion), ma’ana an baiwa motar muhimmanci.
3. Ya kamata a ce Hussaini ya dage kan yarda ya sa hannu a takardar maimakon a ce lokaci kankane ya yarda tun da ya tabbatar ba shi ya yi mata cikin ba.
4. Sunan fim din yana da nasaba da auren Fatima da Hussaini bayan mutuwar yayansa Hassan wadda ba shi ne tushen fim din ba, ya dace a ce sunan fim din yayi kama da ‘Ana zaton wuta a makera’.
5. Ba inda aka nuna iyayen Fatima ko daya duk da ba shi ne jigon fim din ba domin su tirje don fito da hukumcin yin auren tsakanin Hussaini da Fatima.

Matsayi: Zan iya baiwa fim din taurarin girma 4 daga cikin 5.