Monday, August 11, 2008

SHARHIN AL-AMEEN

SHARHIN AL-AMEEN
Daga
Yusuf Ubale

Sunan Fim : Al-Ameen
Kamfani: I.S.I. Films Kano
Shiryawa: Saminu Isah Gidan Shanu
Umarni: Ishaq Sidi Ishaq
‘Yan wasa: Ishaq Sidi Ishaq, Hauwa Ali, Shehu Hassan Kano, Saratu Gidado, Alh.Aminu Hudu, Tanimu Akawu, Ummi Ibrahim, Umar Faruk, Bilkisu Jibrin,A’isha Abdullahi, Tukur S. Tukur, Sani Garba, Bashir Bala Ciroki dss.

Labari
Hausawa suna cewa gaskiya dokin karfe don kuwa duk wanda ya tsaya kan gaskiya to tabbas ko-ba-dade ko ba-jima ba zai tozarta ba. Labarin wani matashin ma’aikaci ne mai suna Al-Ameen (Ishaq Sidi Ishaq) wanda ke kokarin ganin ya rike aikin da yake yi bisa amana tare da tabbatar da cewar bai ci wannan amana dake hannunsa ba. Yana da mata mai suna Balaraba(A’isha Abdullahi), iyayensa da kanensa wanda ya hada da Jamilu (Umar Farouq). Matar tasa dai tana fama da ciwon ‘Asthma’ wadda a dalilin kiransa da kanwarta Amina(Bilkisu Jibrin) tayi cewar ciwon matar ya tashi ya manta a kidime ya bar makullin motarsa a jiki a sakamakon haka aka sace motar.
A wajen aiki shugabanninsa sukan yi kokarin ganin cewar sun yi amfani da shi don cutar gwamnati a matsayinsa na ‘accountant’ a ma’aikatar, wanda duk wata cuta ta kudi sai da sa hannunsa ne za ta yiwu. Al-Ameen yana iya kokarinsa wajen ganin ya tabbatar da gaskiya a cikin aikinsa na gwamnati wanda kila shi yasa ake kiransa da wannan suna. To ganin suna takura masa kan irin wannan bukata tasu kuma kila ganin masu gaskiya a ma’aikatar suna karanci ya rubuta takarda ta barin aiki. A wani lokaci suka kirawo shi domin neman hadin kansa. Lokacin da yazo sun bukaci hadin kan nasa amma ya ki don haka suka dauko takardar korarsa daga aiki a inda shima nan take ya fito da tasa takardar ta barin aiki daga aljihu ya mika musu.
A bangare daya kuma a wani gida an nuna yadda wata matar aure mai suna Zubaida (Ummi Ibrahim) take dawowa daga yawon gararinta inda mijinta (Aminu Ahlan) ke tsaye a kofar gida yana jiran dawowarta. Tana zuwa ya fara nuna mata rashin gamsuwarsa da irin halayenta na yawace-yawace. Ita kuma ta tsagalgale da cewar kada ya takura mata domin tana da ‘yancin fita duk lokacin da taga dama. Daga dukkan alamu ita ta aure shi tunda ita ‘yar masu kudi ce. A nan yake cewar to zai koreta ta bar masa gida ita kuma take fada masa cewar ai gidan ubanta ne don haka sai dai ya fice ya bar mata gidan. Akan haka ta tafi wurin ubanta Alhaji Ghali (Alh. Aminu Hudu) wanda hamshakin mai kudi ne take fada masa cewar mijinta ne ya sako ta. Anan ya dau waya zai buga masa sai gashi ya shigo don haka yake fada masa abinda ‘yarsa take fada, shi kuma ya karyata ta. Don son da uban yake mata nan take ya nuna rashin gamsuwarsa da matakin mijin inda ya bukaceshi daya fice masa daga gida kuma ya ajiye masa mukullin motar da yake hawa.
To shi kuma Al-Ameen ya koma gida inda yake bayyanawa iyayensa (Isah Ja da Hajara Usman) cewar ya bar aiki. Sun nuna damuwarsu to amma sun hakura da matakin daya dauka. Duk da wannan rashin aiki nasa yaci gaba da taimakon iyalinsa da kuma kaninsa Jamilu. A yawonsa na tunanin matakin da zai dauka, yana yawo a kasa har wata yarinya ta fantsama masa ruwa da ta taka da motarta. Ta dan gotashi sannan ta tsaya. Ya nuna bacin ransa inda take ta fiddo da kudi ta danka masa cewar yaje ya wanke. Nan ta bar shi amma fa shi ya rike abin a zuciyarsa. Wannan yarinya itace Zubaida ‘yar wancan attajiri wato Alhaji Ghali.
Alhaji Ghali mutum ne mai yawan kyauta da sadaka domin har zagawa yake da tarin abinci a mota a-kori-kura yana rabawa sa’annan ga taimakon al’ummar da ke bukatar hakan. Amma kash! Idan gizo ke sakar shine duk da wannan hali na Alhaji Ghali ashe yana da matsala babba domin kuwa yana kiran matan mutane daga gidajen aurensu wadda wata gurguwar kawaliya wato Barakah (Saratu Gidado) ke zagayawa tana kawalancinsu. Yau ta nemo masa wannan gobe waccan. Har akwai wacce tana zaune tana tusa kudin da ta samu mijinta ke shigowa inda take yi masa karyar cewar kudin adashinta ne ta karbo har ta bashi wadansu kudin.
A daya fuskar ta Alhaji kuwa yaci gaba da taimakon da ya saba. Wadansu mutane daga wata unguwa Malam Isah da Malam Uba sun je wurin sa neman taimakon karasa masallacinsu wanda suka kasa karasawa. Anan ya nemi jin yawan kudin su kuma suka fada masa cewar Naira Dubu Dari Daya ne nan take ya bada umarnin aje a basu Naira Dubu Dari Biyu, kuma abokinsa (Shehu Hassan Kano) shima ya bayar da nasa taimakon. Bayan haka aka bukace su da su turo yaransu domin daukarsu aiki a kamfanonin Alhajin.
Bayan barinsu sai mahaifin Al-Ameen ya shaida masa cewar ya shirya yaje kamfanin Alhaji Ghali domin za’a dauke shi aiki. Ya dan so ya nuna rashin gamsuwarsa amma dai ya hakura ya shirya ya tafi. A wurin ganawa da shi an fayyace irin burin Alhajin na yin amfani da wadannan matasa domin cimma manufarsa ta safarar wadansu abubuwa na cutarwa zuwa wadansu kasashe. Kuma sauran matasan sun yarda illa shi Al-Ameen wanda take ya nuna cewar shi ba zai yi ba. Sun nuna masa cewar bai isa ba tun da sun riga sun bayyana masa asirinsu. Shi kuma ya fada musu cewar ba zai yi ba. Suka nuna masa cewar to lallai akwai matakin da zasu dauka.Ya dai fice yayi tafiyarsa.
Shi kuma Jamilu wato kanin Al-Ameen kwatsam sai gashi ya sai mota duk da ba aikin da yake yi, hasali ma a wurin yayansa yake samun abin batarwa. Lokacin da iyayen Al-Ameen suka nuna masa motar ya fara tambayar kanin nasa inda ya samu kudin sayen mota, iyayen suka nuna cewar ai arziki nufi ne na Ubangiji don haka ya rufe bakinsa. Ashe da Walakin wai goro a miya domin Jamilu dai ya samu matar da take bashi kudi ne shi kuma yana cika mata bukatarta. Wannan mata itace matar Alhaji Ghali Safara’u (Hawwa Ali Dodo) wanda shima yake bin matan aure ashe shima tasa matar aikinta kenan. Bayan motar daya saya ta kuma bukaci da su tafi hutu Ingila.
Bayan kin da Al-Ameen yayi na karbar irin aikin Alhaji Ghali can kuma matarsa wato Balaraba ta hadu da Barakah wato kawaliyar Alhaji. To ita ma ga dukkan alamu tarkon ya kusa kamata. Kila da alama sai a kashi na biyu.
Shi kuma Al-Ameen ya rama abin da Zubaida tayi masa domin ya shasshafa mata bakin mai a jikin mota da kuma watsa mata wani a jiki kuma ya bata kudi taje ta wanke. A haka dai soyayya ta kullu tsakaninsu.
Alhaji Ghali ya fito da maitarsa afili domin ya nuna yana son takarar gwamna. Don haka ya dauki hayar matasa domin lika fostar sa a ko ina. Ana likawa wasu kuma suna yagewa har abin ya dami mukarrabansa suka gano cewar Al-Ameen ne mai wannan aiki. To an bayar da kwangilar kawo shi kuma har ‘yan banga sun kamo shi suka sako a cikin buhu. Aka dauke shi sai gidan Alhaji aka fito dashi don zartar masa da hukumci. Ana fito dashi Zubaida ta fara kukan kada ayi masa komai nan ta kwace shi zasu fice daga gidan.
Wannan shine labarin kashin farko na Al-Ameen kuma hakika ya tabo wani bangare na rayuwa wanda ya hada da matsalar rayuwar yau da kullum, karancin rikon amana ta aiki musamman aikin gwamnati, kwadayin samun abin hannu ga matasa maza da mata musamman matan aure tare da halayyar masu kudi a cikin wannan al’umma wajen aikata ayyukan masha’a, taimako amma ba tsakani da Allah ba tare da neman mulki ko ta wane hali.
Kamar yadda aka san kamfanin I.S.I. da kuma darakta Ishaq Sidi Ishaq dgk ana samun ingantattun wasanni masu ma’ana da fitar da sakon da ake bukata. Ba sai an bayyana irin finafinansu ba to amma labarin wannan fim Al-Ameen yayi a lokacin da ake karancin fasahar zakulo labari mai ma’ana koda kuwa za a hada da soyayya a ciki.

Nasarori
1. An nuna irin yadda ya kamata wajen rikon amana a wuraren aiki.
2. Illar auren irin matan da ke nuna su ‘yan wani ajin ne da ban.
3. Nuna dogaro da kai ta hanyar yin sana’o’i koda irin wacce Dan Dugaji, ciroki da SK suke yi ne a fim din.Hakika wakar da suka yi tayi dadi ga kuma sako da ke cikinta.
4. Yadda saboda son kudi musamman mata kan fada tarkon Alhazai irin su Alhaji Ghali.
5. Fito da halayen mutane irin su alhaji Ghali da maitarsu wajen neman mulki.

Kurakurai
Akwai ‘yan kurakurai a wannan fim duk da cewar a fasahance darakta, ‘yan wasa da sauran wadanda suka yi shi sun cancanci yabo domin umarni yayi kuma ‘yan wasa sun bi umarnin. Kadan daga matsalolin fim din sun hada da:
1. Ta yaya Al-Ameen ya samu irin gidan da yake ciki? ga kuma motoci bayan albashin sa bai taka kara ya karya ba, musamman a tsari irin na yau a kasarnan gashi kuwa an shaide shi da gaskiya da rikon amana.
2. Irin taimakon da Alhaji yake yi ya kusa yayi yawan da yarda da halayensa na boye zai yi wuya musamman ga mutanen da yake yiwa kyauta da sadaka. A shari’ance wannan zai iya jefa shakku a zukatan mutane game da masu kudi koda kuwa suna kyautatawa.
3. Duk da yana da mummunan zato ga Alhaji Ghali amma bai kamata Al-Ameen ya je ganawa da su sanye da gilashin ido ba domin hakan na nuna bashi da ladabi duk kuwa da yasan halayen Alhajin.
4. Ta yaya ko kuma yaushe su sauran masu neman aikin suka san irin aikin da zasu yi amma shi sai lokacin da yazo ganawar ya sani?
5. Ya kamata ace a lokacin da yake fama da rashin aiki rashin lafiyar matarsa ya tashi domin gwada tsayuwarsa kan gaskiya ta kin karbar wani abu daga hannun mutane irin Alhaji Ghali.
6. Ta yaya yake samun kudin da yaci gaba da harkokins na yau da kullum tunda babu alamar an biya shi kudin sallama daga aiki?

Me zai faru?
1. Mun ga anyi waka tsakanin Al-Ameen da ‘yar Alhaji, shin zasu yi soyayya ne ? Idan zasu yi zata dore ne?
2. Alhaji zai fito takarar gwamna. Yana taimakon jama’a yadda zasu iya goyon bayansa. Kadan ne suka san illolinsa. Shin ya za’a warware wadannan matsaloli?
3. Yaya matsayin “Sugar Mummy” ta Jamilu. Asirinsu zai tonu ko kuwa?
4. Yaya Baraka wato kawaliyar Alhaji zata kasance?
5. Ya kamata a ga ci gaban masu aikin dibar ‘oga’ don nuna ribar dogaro da kai tare da kaskantar da masu handame kudaden gwamnati a kashi na biyu.
Wadannan tambayoyi dama wadansu ya kamata aga amsar su a kashi na biyu.
Jinjina ga Dan Kwalisa domin hoto sauti da sauransu sun yi.

No comments: