Monday, August 11, 2008

SHARHIN AL-AMEEN

SHARHIN AL-AMEEN
Daga
Yusuf Ubale

Sunan Fim : Al-Ameen
Kamfani: I.S.I. Films Kano
Shiryawa: Saminu Isah Gidan Shanu
Umarni: Ishaq Sidi Ishaq
‘Yan wasa: Ishaq Sidi Ishaq, Hauwa Ali, Shehu Hassan Kano, Saratu Gidado, Alh.Aminu Hudu, Tanimu Akawu, Ummi Ibrahim, Umar Faruk, Bilkisu Jibrin,A’isha Abdullahi, Tukur S. Tukur, Sani Garba, Bashir Bala Ciroki dss.

Labari
Hausawa suna cewa gaskiya dokin karfe don kuwa duk wanda ya tsaya kan gaskiya to tabbas ko-ba-dade ko ba-jima ba zai tozarta ba. Labarin wani matashin ma’aikaci ne mai suna Al-Ameen (Ishaq Sidi Ishaq) wanda ke kokarin ganin ya rike aikin da yake yi bisa amana tare da tabbatar da cewar bai ci wannan amana dake hannunsa ba. Yana da mata mai suna Balaraba(A’isha Abdullahi), iyayensa da kanensa wanda ya hada da Jamilu (Umar Farouq). Matar tasa dai tana fama da ciwon ‘Asthma’ wadda a dalilin kiransa da kanwarta Amina(Bilkisu Jibrin) tayi cewar ciwon matar ya tashi ya manta a kidime ya bar makullin motarsa a jiki a sakamakon haka aka sace motar.
A wajen aiki shugabanninsa sukan yi kokarin ganin cewar sun yi amfani da shi don cutar gwamnati a matsayinsa na ‘accountant’ a ma’aikatar, wanda duk wata cuta ta kudi sai da sa hannunsa ne za ta yiwu. Al-Ameen yana iya kokarinsa wajen ganin ya tabbatar da gaskiya a cikin aikinsa na gwamnati wanda kila shi yasa ake kiransa da wannan suna. To ganin suna takura masa kan irin wannan bukata tasu kuma kila ganin masu gaskiya a ma’aikatar suna karanci ya rubuta takarda ta barin aiki. A wani lokaci suka kirawo shi domin neman hadin kansa. Lokacin da yazo sun bukaci hadin kan nasa amma ya ki don haka suka dauko takardar korarsa daga aiki a inda shima nan take ya fito da tasa takardar ta barin aiki daga aljihu ya mika musu.
A bangare daya kuma a wani gida an nuna yadda wata matar aure mai suna Zubaida (Ummi Ibrahim) take dawowa daga yawon gararinta inda mijinta (Aminu Ahlan) ke tsaye a kofar gida yana jiran dawowarta. Tana zuwa ya fara nuna mata rashin gamsuwarsa da irin halayenta na yawace-yawace. Ita kuma ta tsagalgale da cewar kada ya takura mata domin tana da ‘yancin fita duk lokacin da taga dama. Daga dukkan alamu ita ta aure shi tunda ita ‘yar masu kudi ce. A nan yake cewar to zai koreta ta bar masa gida ita kuma take fada masa cewar ai gidan ubanta ne don haka sai dai ya fice ya bar mata gidan. Akan haka ta tafi wurin ubanta Alhaji Ghali (Alh. Aminu Hudu) wanda hamshakin mai kudi ne take fada masa cewar mijinta ne ya sako ta. Anan ya dau waya zai buga masa sai gashi ya shigo don haka yake fada masa abinda ‘yarsa take fada, shi kuma ya karyata ta. Don son da uban yake mata nan take ya nuna rashin gamsuwarsa da matakin mijin inda ya bukaceshi daya fice masa daga gida kuma ya ajiye masa mukullin motar da yake hawa.
To shi kuma Al-Ameen ya koma gida inda yake bayyanawa iyayensa (Isah Ja da Hajara Usman) cewar ya bar aiki. Sun nuna damuwarsu to amma sun hakura da matakin daya dauka. Duk da wannan rashin aiki nasa yaci gaba da taimakon iyalinsa da kuma kaninsa Jamilu. A yawonsa na tunanin matakin da zai dauka, yana yawo a kasa har wata yarinya ta fantsama masa ruwa da ta taka da motarta. Ta dan gotashi sannan ta tsaya. Ya nuna bacin ransa inda take ta fiddo da kudi ta danka masa cewar yaje ya wanke. Nan ta bar shi amma fa shi ya rike abin a zuciyarsa. Wannan yarinya itace Zubaida ‘yar wancan attajiri wato Alhaji Ghali.
Alhaji Ghali mutum ne mai yawan kyauta da sadaka domin har zagawa yake da tarin abinci a mota a-kori-kura yana rabawa sa’annan ga taimakon al’ummar da ke bukatar hakan. Amma kash! Idan gizo ke sakar shine duk da wannan hali na Alhaji Ghali ashe yana da matsala babba domin kuwa yana kiran matan mutane daga gidajen aurensu wadda wata gurguwar kawaliya wato Barakah (Saratu Gidado) ke zagayawa tana kawalancinsu. Yau ta nemo masa wannan gobe waccan. Har akwai wacce tana zaune tana tusa kudin da ta samu mijinta ke shigowa inda take yi masa karyar cewar kudin adashinta ne ta karbo har ta bashi wadansu kudin.
A daya fuskar ta Alhaji kuwa yaci gaba da taimakon da ya saba. Wadansu mutane daga wata unguwa Malam Isah da Malam Uba sun je wurin sa neman taimakon karasa masallacinsu wanda suka kasa karasawa. Anan ya nemi jin yawan kudin su kuma suka fada masa cewar Naira Dubu Dari Daya ne nan take ya bada umarnin aje a basu Naira Dubu Dari Biyu, kuma abokinsa (Shehu Hassan Kano) shima ya bayar da nasa taimakon. Bayan haka aka bukace su da su turo yaransu domin daukarsu aiki a kamfanonin Alhajin.
Bayan barinsu sai mahaifin Al-Ameen ya shaida masa cewar ya shirya yaje kamfanin Alhaji Ghali domin za’a dauke shi aiki. Ya dan so ya nuna rashin gamsuwarsa amma dai ya hakura ya shirya ya tafi. A wurin ganawa da shi an fayyace irin burin Alhajin na yin amfani da wadannan matasa domin cimma manufarsa ta safarar wadansu abubuwa na cutarwa zuwa wadansu kasashe. Kuma sauran matasan sun yarda illa shi Al-Ameen wanda take ya nuna cewar shi ba zai yi ba. Sun nuna masa cewar bai isa ba tun da sun riga sun bayyana masa asirinsu. Shi kuma ya fada musu cewar ba zai yi ba. Suka nuna masa cewar to lallai akwai matakin da zasu dauka.Ya dai fice yayi tafiyarsa.
Shi kuma Jamilu wato kanin Al-Ameen kwatsam sai gashi ya sai mota duk da ba aikin da yake yi, hasali ma a wurin yayansa yake samun abin batarwa. Lokacin da iyayen Al-Ameen suka nuna masa motar ya fara tambayar kanin nasa inda ya samu kudin sayen mota, iyayen suka nuna cewar ai arziki nufi ne na Ubangiji don haka ya rufe bakinsa. Ashe da Walakin wai goro a miya domin Jamilu dai ya samu matar da take bashi kudi ne shi kuma yana cika mata bukatarta. Wannan mata itace matar Alhaji Ghali Safara’u (Hawwa Ali Dodo) wanda shima yake bin matan aure ashe shima tasa matar aikinta kenan. Bayan motar daya saya ta kuma bukaci da su tafi hutu Ingila.
Bayan kin da Al-Ameen yayi na karbar irin aikin Alhaji Ghali can kuma matarsa wato Balaraba ta hadu da Barakah wato kawaliyar Alhaji. To ita ma ga dukkan alamu tarkon ya kusa kamata. Kila da alama sai a kashi na biyu.
Shi kuma Al-Ameen ya rama abin da Zubaida tayi masa domin ya shasshafa mata bakin mai a jikin mota da kuma watsa mata wani a jiki kuma ya bata kudi taje ta wanke. A haka dai soyayya ta kullu tsakaninsu.
Alhaji Ghali ya fito da maitarsa afili domin ya nuna yana son takarar gwamna. Don haka ya dauki hayar matasa domin lika fostar sa a ko ina. Ana likawa wasu kuma suna yagewa har abin ya dami mukarrabansa suka gano cewar Al-Ameen ne mai wannan aiki. To an bayar da kwangilar kawo shi kuma har ‘yan banga sun kamo shi suka sako a cikin buhu. Aka dauke shi sai gidan Alhaji aka fito dashi don zartar masa da hukumci. Ana fito dashi Zubaida ta fara kukan kada ayi masa komai nan ta kwace shi zasu fice daga gidan.
Wannan shine labarin kashin farko na Al-Ameen kuma hakika ya tabo wani bangare na rayuwa wanda ya hada da matsalar rayuwar yau da kullum, karancin rikon amana ta aiki musamman aikin gwamnati, kwadayin samun abin hannu ga matasa maza da mata musamman matan aure tare da halayyar masu kudi a cikin wannan al’umma wajen aikata ayyukan masha’a, taimako amma ba tsakani da Allah ba tare da neman mulki ko ta wane hali.
Kamar yadda aka san kamfanin I.S.I. da kuma darakta Ishaq Sidi Ishaq dgk ana samun ingantattun wasanni masu ma’ana da fitar da sakon da ake bukata. Ba sai an bayyana irin finafinansu ba to amma labarin wannan fim Al-Ameen yayi a lokacin da ake karancin fasahar zakulo labari mai ma’ana koda kuwa za a hada da soyayya a ciki.

Nasarori
1. An nuna irin yadda ya kamata wajen rikon amana a wuraren aiki.
2. Illar auren irin matan da ke nuna su ‘yan wani ajin ne da ban.
3. Nuna dogaro da kai ta hanyar yin sana’o’i koda irin wacce Dan Dugaji, ciroki da SK suke yi ne a fim din.Hakika wakar da suka yi tayi dadi ga kuma sako da ke cikinta.
4. Yadda saboda son kudi musamman mata kan fada tarkon Alhazai irin su Alhaji Ghali.
5. Fito da halayen mutane irin su alhaji Ghali da maitarsu wajen neman mulki.

Kurakurai
Akwai ‘yan kurakurai a wannan fim duk da cewar a fasahance darakta, ‘yan wasa da sauran wadanda suka yi shi sun cancanci yabo domin umarni yayi kuma ‘yan wasa sun bi umarnin. Kadan daga matsalolin fim din sun hada da:
1. Ta yaya Al-Ameen ya samu irin gidan da yake ciki? ga kuma motoci bayan albashin sa bai taka kara ya karya ba, musamman a tsari irin na yau a kasarnan gashi kuwa an shaide shi da gaskiya da rikon amana.
2. Irin taimakon da Alhaji yake yi ya kusa yayi yawan da yarda da halayensa na boye zai yi wuya musamman ga mutanen da yake yiwa kyauta da sadaka. A shari’ance wannan zai iya jefa shakku a zukatan mutane game da masu kudi koda kuwa suna kyautatawa.
3. Duk da yana da mummunan zato ga Alhaji Ghali amma bai kamata Al-Ameen ya je ganawa da su sanye da gilashin ido ba domin hakan na nuna bashi da ladabi duk kuwa da yasan halayen Alhajin.
4. Ta yaya ko kuma yaushe su sauran masu neman aikin suka san irin aikin da zasu yi amma shi sai lokacin da yazo ganawar ya sani?
5. Ya kamata ace a lokacin da yake fama da rashin aiki rashin lafiyar matarsa ya tashi domin gwada tsayuwarsa kan gaskiya ta kin karbar wani abu daga hannun mutane irin Alhaji Ghali.
6. Ta yaya yake samun kudin da yaci gaba da harkokins na yau da kullum tunda babu alamar an biya shi kudin sallama daga aiki?

Me zai faru?
1. Mun ga anyi waka tsakanin Al-Ameen da ‘yar Alhaji, shin zasu yi soyayya ne ? Idan zasu yi zata dore ne?
2. Alhaji zai fito takarar gwamna. Yana taimakon jama’a yadda zasu iya goyon bayansa. Kadan ne suka san illolinsa. Shin ya za’a warware wadannan matsaloli?
3. Yaya matsayin “Sugar Mummy” ta Jamilu. Asirinsu zai tonu ko kuwa?
4. Yaya Baraka wato kawaliyar Alhaji zata kasance?
5. Ya kamata a ga ci gaban masu aikin dibar ‘oga’ don nuna ribar dogaro da kai tare da kaskantar da masu handame kudaden gwamnati a kashi na biyu.
Wadannan tambayoyi dama wadansu ya kamata aga amsar su a kashi na biyu.
Jinjina ga Dan Kwalisa domin hoto sauti da sauransu sun yi.

SHARHIN FIM DIN FASSARA 1 & 2

SHARHIN FIM DIN FASSARA 1 & 2
Daga
Yusuf Ubale

Sunan Fim: Fassara
Kamfani: Al’umma Production
Daukar Nauyi: Gali Lawan Zango
Umarni: Ashiru Nagoma
Masu fadakarwa: Shehu Hassan, Kabiru Nakwango, Bashir Nayaya, Ali Nuhu, Ashiru Nagoma, Adamu A. Zango, Hafsa Shehu, Rukayya Umar, Aina’u Ade, Mansura Isah,Jamila Haruna dss.

‘Duniya susar jaki ce, yi mini nai maka. Kowaye a duniya idan yayi sai anyi masa. Duk mutumin daya tsallaka katangar wani ko ya tsugunna akan katangar wani yayi kashi to sai an ketara tasa ko an masa kashi shima. Idan kayi a katangar mutum kwaya daya, goma sai sun yi a taka.” Kabiru Nakwango a cikin fim din Fassara 2.
A wannan karon ina son zanyi sharhi ne akan fim guda daya amma kashi na daya dana biyu. Ban sani ba ko an yi sharhin na dayan to amma saboda sako da muhimmancin wannan fim tare kuma da samun cikakken bayani shine dalilin hadawa domin hasko irin hasken da wannan fim yake koyarwa.
Kashi na farko
Labarin ya fara ne da nuno wani Alhaji (Shehu Hassan) yana zaune da ‘yarsa Lubna (Hafsa Shehu) wacce mahaifiyarta ta rasu ta bari tare da uban da kuma yayanta Babangida (Ashiru Nagoma). To shi dai mahaifin nasu saboda dalilin da shi kadai ya sani ya ki sake wani auren bayan rasuwar ita mahaifiyar ‘ya’yan nasa. Ita Lubna ta girma yadda har ta isa aure amma saboda wani dalili da kuma hankoronsa na son ganin ta auri mai hannu da shuni yasa ya ajiyeta a gabansa duk da irin matsin lamba da yake samu daga surukansa (Kabiru Nakwango da Jamila Haruna) da suke ta hura masa wuta kan ganin ya aurar da ita domin barinta haka bai dace ba. Sun nuna masa tunda dai ga manemi ta samu ai kawai sai ayi. Amma shi ya tsaya tuburan cewar shi yaron da yake nemanta fa wato Nasir (Ali Nuhu) ba wani abu gare shi ba domin a wuri daya suke aiki yasan shi. Shi kawai sai ya samu wanda a ganinsa ya dace da ‘yarsa.
Kamar yadda koyarwa addinin Musulunci da al’adar Hausa take koyarwa zaman da yake shi da ‘yarsa yana da hadari. Wannan zama yasa ya kyasa irin yadda take musamman idan taci ado da irin kananan kayan nan na zamani. Ko da yaushe tana gilmawa ta gabansa, ta dafa musu abinci, kai a takaice suna zaune su kadai a gidan. A irin haka dai har akwai lokacin da ta fito zata shiga bayan gida shi kuma yana zaune a falo ya tambaye ta me zata yi. Ta fada masa, yace ai sai tayi amfani da na falon. Don haka tana shiga ya bita ciki inda abin da zai auku ya faru.
A sakamakon wannan mummunar saduwa da yayi da ‘yarsa ta shiga halin damuwa. Domin hakika ita ta tabbatar wannan abu bai dace ba. Sakamakon dai wannan haduwa juna biyu ya shiga wato ta samu ciki.
Shi kuma Nasir ya dage ganin lallai sai ya kara aure musamman Lubna wacce suka shaku duk da wulakancin da mahaifinta yake yi masa. Kuma hakika ya gamu da gumurzun matarsa wacce ta dorawa kanta bakin kishi. Duk da haka ya tsaya kan bakansa har dai shi uban Lubna ya aurar masa amma ba wai don yaso ba a’a sai dai don ta zama jangwam, kuma ya rufawa kansa asiri kada bakin duniya ya dame shi. Ita kuwa uwar gidansa (Aina’u) ta daura yakin zama da wannan kishiya har dai a karshe ta gano sirrin da ke dabaibaye da Lubna. Ta bayyana masa cewar lallai Lubna da ciki ta shigo gidannan kuma tana da tabbacin haka.
A daya bangaren na mahaifin Lubna, saboda matsin lamba ya cije ya auri wata matar Hafsa (Rukayya Umar). Tarewarta keda wuya; ba a gama cin amarci ba sai tafiya ta kama mijin inda ya bar dansa domin kula da gida da duk wani sha’ani da matar take bukatar yi. Bayan tafiyarsa ita matar ta bukaci dan mijin nata wato Babangida (Ashiru Nagoma) daya taimaka mata da ci gaban karatunta kada ta rika mantawa. Shi kuma ya yarda da haka. To amma ita da dalilinta ko manufa na wannan bukata. Domin ta fito da maitarta a fili lokacin da ta nemi su yi shedana kuma nan ma shaidan ya samu cin nasara. Tayi amfani da kissa da jan hankali irin wadda take da ita har ya yarda.
Jin dadin da yayi a karonsu na farko shima yaga ya kamata ya ci gaba da darjewarsa. A takaice dai sun sake fadawa cikin wannan aika-aika katsam sai ga mijinta kuma mahaifinsa ya fado dakin ya same su a cikin wannan mummunan hali.

Kashi na Biyu
To sakamakon abinda ya tarar a gidansa tsakanin dansa da amaryarsa nan da nan ya dau matakin korar dan daga gidan. Mahaifinsa ya nemi jin dalilin korar dan da ya haifa daga gidan to amma ya kasa fitowa fili ya bayyana dalilin hakan. To itama dai matar tasa a karakaunar da suka sha ita da dan mijinta, ciki ya samu.
Nasir kuwa ya lura da maganar matarsa inda ya tabbatar da haka a lokacin daya kira Lubna domin jin yadda akayi. Ya bayyana irin soyayyar da yake yi mata amma hakika bashi da wani zabi illa su rabu domin Allah Ya hana auren mace da ciki. To ita dai saboda tsagwaron gaskiyarta ta amsa cewa lallai da ciki ta zo gidan kuma hakika shari’a bata yarda da boye gaskiya ba. Kawai abinda ya dace shine ya dau duk matakin daya yaga dace kamar yadda take gaya masa. To matakin daya dauka shine yi mata saki har uku gaba daya. Amma dai yayi mata nasihar cewar ta lura da duniya, idan kuma da rabon su sake haduwa to shikenan. Suka dai rabu.
Abin boye dai ya fito fili domin maganar cikin da yayi ma ‘yarsa ta fito kowa yasan abin daya wakana. Surukinsa (Kabiru Nakwango) ya zo wurinsa kuma ya fatattake shi da zafafan maganganu kan irin aika-aikar daya aikata. Ya bayyana masa irin zubar da kimarsa da yayi a gaban ‘yarsa da kuma zubar da mutuncin kansa da yayi a idon duniya sakamakon wannan abin tir da yayi. Ya nuna cewar lallai ya zama kwaro, ya zama cinnaka wadda ko a wurin yara sai dai a mitsittsike, ya zama jaba da gizo-gizo kuma ya zama mujiya a cikin tsuntsaye. Mutunci dai ya zube.
Shi kuwa Nasir bayan ya saki Lubna sai Allah Ya hada shi da wata kanwar kawar matarsa lokacin da ta zo domin isar da sako ga matarsa. Ganinsa keda wuya ta fada kogin kaunarsa. Kuma dai a takaice ya aureta duk da matsayin matar tasa bayan yayi mata wayon tura ta kasa mai tsarki kafin ta dawo anyi auren.
Shi kuma Babangida ya bayyana ma kanwarsa dalilansa na aikata aika-aikar da yayi da matar mahaifinsa bayan ita kanwar ta tambayeshi abinda yasa yayi hakan. Ya nuna cewar gaskiya yaji zafin abin da mahaifinsa yayi mata don haka shi yana ganin ya mayar da martani ne kuma ya dauko fansa ne, kuma a ganinsa bai yi wani laifi ba.
Lubna dai saboda zafin abubuwan dake damun ta har kusan ta daina tsoron mahaifinta. Ta fito balo-balo ta gaya masa cewar mijinta ya sake ta kuma ya saurari baragurbin day a fashe a gidansa. Ta bayyana masa cewar kazantar tayi yawa, uba da ‘yarsa.
Gida dai ya zama wani hargitsattse. ‘Ya dauke da cikin da ubanta yayi mata, Mata da cikin da dan mijinta yayi mata. Amma dai ya nemi da matar tasa ta zubar da cikin amma ta tsaya kai da fata cewar lallai sai ta haife. Yadda kowa ya taka kasa haka abinda yake cikinta sai ya taka kasa.
Alhaji kuma ya sake neman wata bazawara (Hajara Usman). To amma zaman bai karko ba saboda samun labarin da tayi na irin abinda ya shafeshi. Ta gaya masa cewar ita tunda take bata taba ganin irin wannan kwado ba; yayiwa ‘yarsa ciki sa’annan dansa yayiwa matarsa cikin. Don haka ta bashi kwanaki uku kan ya sallameta.
A kwana a tashi dai abin boye ya fito fili domin dole aika-aikar ta fito. Lubna da matar mahaifinta sun haihu. Gida ya zama wani iri. Akan tilas Alhaji yake daukar ‘yarsa kuma jika, shi kuma Babangida ya dau dan da matar babansa ta Haifa amma daga gareshi (Babangida).
A karshe dai surikin Alhaji ya tattaro wadanda abin ya shafa wato Alhaji, Lubna, Babangida da Nasir inda ya ragargaji yadda Alhajin ya sha batawa Nasir kan nemen Lubna sai da ta kwabe sa’annan ya lallaba ya bashi ita da aure.
A wannan zama dai an fayyace duk abubuwan da suka faru kuma Alhaji yayi nadamar abinda ya aikata. Don haka surukinsa ya bukace shi da ya nemi gafarar ubangiji da kuma korar gaba bisa sharadin cewar yabi ka’idar tuba wato yin nadama da kuma kudurcewa a zuci ba za’a kara aikatawa ba.
Karshen fim din Fassara kenan.

Sharhi
Hakika wannan fim ya tabo wata babbar matsala kuma annoba da tayi katutu a wadansu gidajen musamman masu kwadayin son abin duniya. Ya nuna irin sakacin wadansu iyayen wajen zama da ‘ya’yansu mata ba tare da wani a tare da su ba. Wannan fim ya nuna shiga hadarin irin wannan zama. Tabbas duk mutumin daya zauna daga shi sai balagaggiyar ‘yarsa to ya shimfidawa shaidan shimfidar zama a gidansa.
Wannan fim ya nuna cewar tabbas, lallai duk abinda mutum ya aikata to ko-bajima-ko-badade sai yaga a kwaryarsa, shima dole ayi masa. Masu hali irin na Alhaji ba zasu ji dadin rayuwarsu ba.
Illar irin wannan hali na kwanciya da ‘ya ko makamancin haka yana da illoli da sakamako da yawa. Ga dai rashin samun sukunin yin aure daga manema, gallazawa daga kishiya ko kawaye, tunanin abinda mutum zai tarar a wurin Ubangijinsa, sa’annan bata zuri’a har abada. Shi kuma mai aikata abin da shi da kwanciyar hankali sun yi sallama. Kullum hankali tashe, hada zuri’a da shi ma jan aiki ne. Kasancewa dan wannan zuri’a ma abin kyama ne kamar yadda Lubna ta yi fatan ina ba a nan gidan Allah Ya halicce ta ba.

Burgewa
Wannan fim babbar fadakarwa ce kuma duk wadanda suke da hannu wajen wannan fim sun cancanci yabo. Kowa yabi irin umarnin da aka bashi musamman Lubna (Hafsa) wacce itace ginshikin duk abinda ya biyo baya. Haka mahaifinta (Shehu Hassan). Allah Ya kara basira amin.
Hakika fim din ya burge. An jawo hankalin masu kallo wajen tsawaita damuwa da Lubna take ciki domin ya kara jan kunne ga mutane masu tunanin aikata irin wannan. Hafsa ta dace da wannan matsayi musamman wajen sanyaya jikin masu kallo.
Yadda Nasir ya nuna tsabagen so gareta amma duk da haka don nunawa jama’a cewar babbar magana ce yasa tilas ya saketa. Matakin daya dauka yana da wuya tunda ya sameta mai kyawun hali. Maganganun da yayi mata lokacin da zai sake ta gaskiya sun ja hankalin mai kallo. Dole ne a jinjina wa mutanen da suke da hannu wajen wannan fim musamman mai bayar da umarni.
Aina’u itama ta nuna irin halin da yawancin matanmu kan nuna musamman idan za ayi musu kishiya. Itama ta burge.
Matsayin Hafsa (Rukayya) ya nuna yadda mata kan yaudari samari domin aikata wata badakala, ta nuna kwarewa wajen hilatarsa domin aikata aikin assha.

'Yan matsaloli
Babban kuskuren wannan fim shine babu wata dangantaka tsakanin rayuwar Mansura da saurayinta da jigon fim din. Ina ganin an dai yi cikon kilo ne don a nishadantar da kuma nuna kwalisa kawai.
Abu na biyu shine kwata-kwata babu muhallin waka da rawa a cikin fim din domin tsabar tausayi da kuma kokarin ganin abinda zai wakana zai sa mai kallo ya tura wakokin fim din gaba.
Lubna tana bayyanawa cewar mahaifinta ya tsare ta har da bindiga idan bata yarda dashi ba, to amma mu mun ga bandaki ya bita har kuma mun ji calla karar da tayi, sai dai watakila ba wannan ne karon farko ba.

Sharhin Fim din Nakiyar Kan Kashi

NAKIYAR KAN KASHI
Kamfani - Al-Khalil Film Productions
Mai shiryawa - Ibrahim Khalil Dan-Shagamu
Umarni - Ahmad S. Alkanawiy
Masu Fadakarwa - Kabiru Maikaba, Umar Bankaura, Bashir Nayaya, Ibrahim Khalil, Hajara Usman, Ladi Mutu-Ka-Raba, Zainab Booth, Binta Mohd, Zainab Ibrahim Kanya, Ummi Ibrahim dss.

Labari
To yau dai a takaice zan bayar da yadda wannan fim yake. Khalil (Ibrahim Khalil) dai dan jarida ne wanda yake gabatar da wani shiri mai farin jini a gidan rediyo. A cikin irin masoyan wannan shiri nasa har da wata yarinya mai suna Zillaziya (Ummi Ibrahim). To soyayya dai ta shiga tsakaninsu kuma har yaje wajenta a gida don tattaunawa da ita kan yiwuwar aurensu.
Khalil ya fara cin karo da matsaloli guda biyu; mahaifinta dai Baba Iro (Bashir Nayaya) abin duniya ne kawai ya rufe masa ido; baya bukatar ganin wani a wurin ‘ya’yansa sai hamshakan masu kudi. A takaice ‘ya’yansa mata jari ne a gareshi; daya matsalar kuma ita ce Zillaziya tana cikin gungun wasu kawaye wadanda suma babu abinda ke gabansu illa su samu kudi ta kowane hali, kuma basa bukatar ganin tayi aure. Don haka wadannan bangarori biyu suna yin barazana ga son dake tsakanin Khalil wanda bai taba aure ba da da Zillaziya wacce take bazawara ce.
Kamar yadda aka san iyayenmu wajen hangen nesa, magabatan Khalil basu so wannan nema ba, musamman irin gaggawar saka auren cikin sati daya ba tare da cikakken bincike da natsuwa ba.
A takaice dai an yi aure. Khalil ya fara fuskantar matsala ta farko ranar da suka tare inda ta nuna masa ita fa tana cikin al’adarta ne. Sauran matsalolin da ta kawo masa sune:
Ba zata rika yin girki ba, sai dai a rika sayowa ko kuma a dauko ‘yar aiki.
Kada ya rika saka mata ido a cikin harkokinta da abokan huldarta maza da mata.
Bata son wa’azi da kuma fada.
To a dai wadannan matsaloli abubuwa suka yi zafi har dai akarshe aure ya mutu.

Fadakarwa
Wannan fim yazo da daya daga cikin matsalolin da suka addabi wannan al’umma. Fadakarwar da fim din yake koyarwa sun hada da:
Labarin yana da muhimmanci domin kaucewa zaben tumun dare.
Yana nuna cewar iyaye suna da babbar gudunmuwa wajen shawartar ‘ya’yansu musamman wajen harkokin neman aure.
Yana nuna irin rikon sakainar kashi da wadansu mata kan yiwa ‘ya’ya musamman mata da aka bar musu.
Yana nuna illar barin ‘ya’ya suyi kawance da wadansu ba tare da cikakken binciken irin kawayen da suke hulda da su.
Son zuciya na jawo rashin kwanciyar hankali.
Muhimmancin zaman aure, domin babu wata kwangila ga mace fiye da gidan miji.
Yana nuna cewar gaggawa musamman a aure aikin shaidan ce.
Uwa-uba, rashin bin shawarar iyaye, rashin natsuwa, rashin bincike duk kan haifar da auren dana-sani har mutum ya dauko nakiyar kan kashi.

Abubuwan Burgewa
Ya kamata a yabawa Ibrahim Khalil wajen zakulo irin matsalolin da suka dabaibaye al’ummarmu. Babbar matsala ce wacce tayi katutu; samari kan yi aure cikin gaggawa ba tare da kwakkwaran bincike ba; mata masu neman aji kan shiga halaka ta hanyar shiga harkoki marasa dadi; iyaye kan mayar da ‘ya’yansu mata haja don neman kudi dasu.
Wani abin kuma shine yadda aka kaucewa rawa da waka marasa amfani. Anyi kokari wajen saka wakoki masu fadakarwa a matakai daban daban da suka dace da yanayin da ake ciki a fim din.

Matsaloli
Kadan daga ckin ‘yan matsalolin wannan fim sune:
Mahaifin Zillaziya yana wuce gona da iri wajen bayyana kwadayinsa a fili ba tare da bi a hankali ba. Da wuya ace mutum mahaifi musamman Bahaushe, Bafillatani ko danginsa su rika yin irin yadda yake yi balo-balo duk da rashin abin hannunsa.
Zai yi wuya ace Khalil ya yarda ya ci gaba da neman Zillaziya musamman a tashin farko daya fara cin karo da matsaloli; ina ma ace ya samu wasu dalilai kwarara daga baya bayan soyayya ta kullu sosai sannan a taka masa burki.
Wani lokaci Khalil idan yana takarkarewa yana magana sai abin ya zama kamar na wasa wato ‘comedy’.
Bai kamata a ce Khalil ya barke da kuka ba duk da sharrin da surukinsa yayi masa. Namiji, dan book kuma wayayye bai kamaci ya barke da kuka don anyi masa irin sharrin da surukinsa yayi masa. Shima wannan kamar wasan ban dariya.
Duk da irin mugwayen halayen da gungun matan suke aikatawa ba a fayyace gaskiyar abin da suke aikatawa ba, sabanin yadda mai fim din ya fada kafin fitowar fim din a wata hira a gidan rediyo (Freedom) inda yake cewar su matan ‘yan madigo ne, amma sai gashi ta kasance kamar suna hulda da masu kudi ne maza a Abuja.
A bangaren Zillaziya, kawayenta, mahaifanta ba a nuna wata fadakarwa da zata zama ishara ga masu irin wadannan halaye ba. Ya kamata ace su ga wata illa da zata sa a kori gaba don mai kallo ya tabbatar cewar tabbas akwai illa wajen aikata hakan.
Khalil bai dau hukumci akan halayen matarsa ba;, ya dai yanke hukumci ne kan dalilin halayen da mahaifinta yake nuna masa kawai. Ya kamata yaga zahirin abubuwan da take aikatawa domin ya guji mai hali irin nata har kuma yayi amfani da filin da yake gabatarwa a rediyo domin fadakar da sauran jama’a domin bin iyaye, bincike domin gudun fadawa tarkon da-na-sani.

SHARHIN FIM DIN RIKOH

Daga
Yusuf Ubale Ajingi

Sunan Fim Rikoh
Kamfani Dutsen Gima Movie Planet/FKD Production
Shiryawa Bashir Muhammed Dutsen Gima
Labari Bashir Muhammed da Ali Ibrahim Khalil
Umarni Ali Nuhu
Shekara 2005
Masu Fadakarwa Ali Nuhu, Jibrin S. Fagge, Saima Mohd,Jamila Haruna, Hajara Usman, Kabiru Nakwango, Shehu Hassan Kano, Bashir Nayaya dss.

Labari
Wannan fim yana tafe da babban sako na nuna yadda riko yake da illa har ya kai mutum ga yin aika-aika.
Labarin wani attajiri d’an kasuwa ne mai suna Alhaji Kabiru (Kabiru Nakwango) wanda yake da k’ok’arin sauk’ak’awa jama’a wajen tabbatar da sayar musu da kaya akan farashi kamar yadda kamfani yake bashi. Hakan da yake yi bai yiwa d’an uwansa kuma abokin huld’ar kasuwancinsa Alhaji Hassan (Shehu Hassan Kano) d’ad’i ba kuma yana ganin wannan zai iya durk’usar da harkokin nasa tun da jama’a zasu bar wurinsa su koma wurin shi Alhaji Kabiru. Yayi k’ok’arin ganin ya jawo hankalinsa kan illar da yake yi masa, shi kuma ya dage kan wannan hali na taimakawa. Matar Alhaji Hassan, Hajiya A’isha (Jamila Haruna) kullum k’ok’arin da take shine na jan hankalin mijinta don daina wannan gaba daya d’aukarwa kansa. A taik’ace shi dai bai ja da baya ba kan ganin karshen abin ba har kuma yake fada mata cewar zai iya daukar kowanne mataki don ganin ya sami galaba.
Akwai lokacin da suka hadu da Alhaji Kabiru inda har yake nuna masa kiri-kiri cewar ba ruwansa dashi tunda niyyarsa yaga ya raba shi da harkokinsa. Alhaji kabiru yayi masa nasiha amma ya tsaya daram kan hakilon da yake yi a inda har yayi barazanar cewar zai iya hallaka shi kan wannan. Alhaji kabiru yayi mamakin wannan lafazi na kisa.
Kwatsam rannan Alhaji Kabiru yana dakinsa yana barci wasu karti suka danne shi suka kashe.
Saboda furucin da yayi na kashe Alhaji kabiru, ai ba wata tababa matarsa Hajiya Hajara (Hajara usman) tare da dansa Abba (Ali Nuhu) suka kai Alhaji Shehu wurin ‘yansanda inda aka fara gana masa azaba domin amsa tuhumar da ake yi masa. Shi kuma ya tsaya tsayin daka cewar ba shi da ruwa wajen wannan kisa.
A wani bangaren kuma kafin rasuwar Alhaji Kabiru saboda kauna da jin dadin kammala karatun dansa Abba, yayi masa albishir da saya masa mota irin wacce yake so. Don haka ya tafi wurin Alhaji Sa’idu (Jibrin S. Fagge) tunda yana sayar da motoci domin ya zaba. Aka gaya masa su zo da mahaifinsa domin zaba. To amma a dalilin tafiya da mahaifin nasa yayi sai mahaifiyarsa tazo.
Suna zuwa sai Hajiya Hajara ta gane shi har take tambayar sa cewa dama yana Kano? Anan dai ta nuna Abba a matsayin danta.
Ba a dade ba aka yiwa Alhaji Kabiru wannan kisan gilla. A bayan nan ne Alhaji Sa’idu ya rika ziyarta Hajiya har yana kyautata mata dai dai gwargwado kuma dama garinsu daya wato Gombe wadda wannan tasa ake tunanin ko ‘yan uwa ne. Ana haka har dai ya nuna maitarsa a fili na son auren ita Hajiya Hajara. Ita kuma ta nuna masa cewar ai ta riga ta yiwa wani aminin marigayin mijinta alkawarin auren sa. Shi kuwa Alhaji sa’idu ya dage kan ko ta hali ka-ka sai ya aureta kuma zai iya aikata komai kan ganin hakan. Ashe da walakin wai goro a miya, ya taba nemanta da aure tun suna matasa amma aka hana shi saboda kamar yadda yace bashi da kudi. Ba a dade da wannan batu ba manemin Hajiya shima ya mutu.
Ana ta jimamin kisan da aka yiwa Alhaji Kabiru sai wani mutum wanda yake abokin Alhaji Sa’idu ne wato Alhaji Ya’u (Bashir Nayaya) ya tseguntawa Abba cewar ga wanda ya kashe mahaifinsa. Nan da nan suka dunguma tare da ‘yan sanda aka kama shi. Duk daya musanta zargin daga baya ya amince kana kuma ya bayyana yadda ya sha fama da masifar son Hajara a can Gombe lokacin suna matasa amma saboda rashin kudi aka hana shi. Shi kuma saboda zuciya nan ya tattara nasa ya nasa ya cilla Ikko da niyyar shi ma sai ya nemo kudin da zai iya aurenta. Ya je kuma ya samo kudin. Sai dai kash! Yana dawowa aka fada masa ai tayi aure kuma suna Kano. Nan yayi niyyar nemota koda zata kai ga kashe wanda ya aureta ne. Wannan shi ya rike a zuciyarsa har bayan shekaru masu yawa ya aiwatar da nufinsa.
Wannan shine labarin wannan fim na Rikoh.

Sharhi
Wannan fim shine na farko da kamfanin Dutsen Gima Movie Planet tare da jagorancin FKD Production ya shirya.
Labarin fim din yana da karfi da sarkakiya tare kuma da jan hankalin mai kallo musamman kan wanda yake da alhakin kashe Alhaji Kabiru domin ganin furucin da Alhaji Hassan ya sha yi kan abubuwan dake tsakanin su. Wannan zai sa mai kallo ya tabbatar cewar lallai shi ya sa aka kashe shi.
Duk da cewar akwai soyayya a cikin wannan fim amma jigon labarin yana nuna yadda riko a zuci kan haddasa aikata wata aika-aika tare kuma da nuna yadda gaba kan kullu kan neman abin duniya musamman harkoki irin na kasuwanci.



Fadakarwa/Burgewa
Masu shirya wannan fim sun yi kokari tunda wannan shine na farko da suka saki. ‘Yan wasa tare da uwa-uba mai bayar da umarni suma sunyi kokari. Kadan daga cikin abubuwan daya kunsa sun hada da:
Amfanin kyautatawa al’umma da iyali.
Illar dagewa wajen aurar da mace ga mai kudi kawai duk daya kamata ace manemin yana da madogara domin kula da matar.
Nuna shawara ta gari daga mace don kwantar da hankalin miji don kada ya aikata aikin dana-sani.
Duk da kusancin abokantaka bai kamata a rika boye mugun sirri ba musammnan idan laifi aka aikata.
Nuna cewar baki shi kan yanka wuya, ma’ana mugun furuci bashi da amfani.
Illar rikon mutum a zuci da irin bala’in da yake jawowa mai irin wannan hali.

Kurakurai/Shawarwari
Duk da kokarin da akayi wajen yin wannan fim akwai ‘yan matsaloli da ba za’a rasa ba da kuma ‘yan shawarwari domin gyaran gaba.
Babu wani sakamako da aka yiwa Alhaji Kabiru a fim din kan irin kyautatawarsa wanda hakan zai karawa masu irin wannan hali azama. Kawai sakamakonsa shine kisan da aka yi masa.
Ya kamata ace bai dau maganar da Alhaji Hassan da wasa ba. Ya kamata ace ya dau mataki ko da ta hanyar tsaron kansa ne ko fadawa hukuma.
Duk da kamun da aka yiwa Alhaji Hassan to amma ba’a san makomarsa ba tunda zai iya yafewa ko kuma ya dau wani mataki musamman irin azabar daya sha a hannun’yan sanda (ko sai a kashi na biyu idan da akwai?)
Soyayyar Abba da Zainab (Saima Muhd) bata da wata dangantaka da fim din.
Haka zalika wakokin da aka saka an yine kawai domin nishadantarwa domin jan hankalin masu kallo tun da cashiya suke bukata.
Ya kamata ace matar Alhaji Hassan ta ja hankalinsa bayan an sallame shi daga wurin ‘yan sanda kan illar irin matsayinsa na gaba da kullatar mutum da kuma fadar Magana ba tare da ja ma bakinsa linzami ba wadda hakan zai kara fadakar da masu kallo. (Watakila sai a kashi na biyu)
Duk da kasancewar kalmar RIKO ta dace da labarin amma wajen rubutawar bai kamata a kara harafin ‘h’ ba. Amma ban san abinda malaman harshen Hausa zasu ce ba.Shawara ta anan shine a daure a rika tuntubar masana harshen domin tabbatar da yadda ake rubuta kalma.
Duk da kauna da Hajiya Hajara take yiwa mijinta sai gashi bayan sati biyu kacal da mutuwarsa an nuno ta tasa talabijin a gaba duk da a lokacin ana cikin alhinin wannan rashi.wadda a al’adar Bahaushe kusan hatta sauraren rediyo ko hayaniya ba a yi sai an dau tsawon lokaci.
Babu wani kokari da akayi wajen nemo masu kisan domin suma a hukuntasu. Kawai sun yi kisa sun kama gabansu sai dai idan za ayi hakan a kashi na biyu in kuma ba haka ba to an daurewa ‘yan ta’adda gindi kenan.
Ya kamata a ce an nuna kwarewa saboda ci gaban zamani wajen zakulo wadanda suka aikata kisan misali ta hanyar daukar hoton hannun masu laifin akan mayafi da filon Alhajin lokacin da suka kashe shi maimakon dogara da shaida ta baki wacce bata da inganci sosai.
Ina fatan za’a samu gyara kan irin wadanda abubuwa da ake samu a cikin finafinan mu.

NEMAN GYARAN HALAYYAR ‘YAN FIM


A kwana a tashi yau gashi an shafe shekara guda da faruwar badakalar Maryam Usman. Allah cikin ikonSa har kuma an samu karuwa. Kowa ya sha fadin ra'ayinsa kan abinda ya faru da kuma hanyoyin da ake ganin zasu kawo gyara. To ni ma a wancan lokaci na fadi ra'ayoyina. Wannan da ke kasa daya ne daga cikinsu domin tunawa da baya wanda Bahaushe ke cewa shine roko.
Ko da yake abinda zai faru ya riga ya faru. Wannan Magana ta dade tana yawo a tsakanin ‘yan industri ta finafinan Hausa. Farkon abin a matsayin jita-jita yake yawo wadda har aka samu watanni. A hankali abin yana yawo har sai yanzu ya bayyana karara. To a gaskiya an fadi ra’ayoyi iri-iri kuma har yanzu wadannan ra’ayoyi basu kare ba. Abinda aka sani dai duk abin ya riga ya faru sai dai neman gyara a gaba. Amma abin bakin ciki ne kuma abin tausayi wanda bai taba faruwa a masana’antar finafinan Hausa ba.
To amma duk da haka fadar ra’ayi ya zama dole. Tun kafin wannan badakala ta wakana ake ta yin korafi game da halayyar ‘yan fim musamman mata. Ta kowanne bangare kalubale ne gasu ‘yan fim to amma matsayinsu shine su dai fadakarwa suke. Sun tsaya akan lallai su masu fadakarwa ne kuma ma ai akwai wadanda suka fi su iskanci a gari suna yawo amma ba wanda yace musu kanzil. Don me su za’a damesu. To an sha samun ra’ayuyyuka kan wannan. Ni ina ganin duk mutumin da yace shi malami ne mai koyar da dalibai ko almajirai ko sauran jama’a to yana tare da sa-ido. Da zarar ya aikata ba daidai ba to jama’a zasu yi masa caa domin shi ya kamata ya nuna yadda ya kamata ayi tarbiyya. Amma wanda halayyarsa dama a fandare take ya zama tantiri to lallai a gari ba a cika damuwa da duk wani iskanci da yayi ba. Ba kuma labari bane a wurin jama’a don yayi hakan.
A rayuwar mu ta yau da kullum kowa ya san irin fasikancin da ake yi. Idan mutum bai gani da idonsa ba to zai ji labari. Kuma muna munafurtar kamu ne domin a wadansu lokutan masu yawan surutun suna wannan aika-aikar to amma bambancin abinda ya faru yanzu shine ya shafi irin wadanda suke cewar su fadakarwa suke kuma an fito da wani tsari na daukar abin a bidiyance a ka kuma yada shi a duniya kowa ya gani. Wannan shine bambancin wannan matsala da abinda yake faruwa. Wadansu wadanda suke farwa Hiyana suma suna da nasu abin asshan ko dai a ciki ko wajen wannan harka.
An sha tattaunawa kuma na taba fada a majalisar finanafin Hausa ta intanet cewar bazan yi mamakin duk abinda ‘yan fim suka aikata ba domin suna yi kuma an sani. Matsalar shine an ki shawo kan abin. Laifin jama’a masu kallonsu ne ko gwamnati ko kuma shugabannin su masu fadakarwar ne. Kai na tabbata akwai abubuwa da aka sha aikatawa wanda ko kare ba zai ci ba amma an ki yin wani abu. Kuma yadda abubuwa suke wucewa sasakai to na tabbata duk hayaniyar da ake yi yanzu idan ba’ayi hankali ba a banza zata wuce kuma zamu gani. Idan kuma ana son ganin rashin faruwar makamancin wannan to mun zubawa shugabannin ‘yan wasan da kuma gwamnati ido.
Shawarwarin da nake dasu kan matakan daya kamata a dauka sun hada da:
Tantance halascin shigowar ‘yan wasa. Misali, kawai sai kaji yarinya tace wai da yardar iyayenta ta shigo bayan karya ce zalla. Idan ma da izinin to zaka tarar mahaifiyarta ce ta amince babu sanin mahaifin domin tare suke da mahaifiyar kila sun rabu da mahaifin na ta ko kuma ya rasu. Ita kuwa saboda rauni irin nasu na son kawa da kyale-kyale sai su kyalesu. Kuma wata da aurenta zata zo amma ba wanda zai bincika sai dai idan mijinta ya zo a yi ta rigima.
Tantace halayyar ‘yan wasa. Mal. Jibrin Fagge ya bayar da misalin zuwan wata daga Nijar ana cikin wannan badakala wai tazo shiga fim. Kawai sai mutum tsilif ya tsallako sakaka yace wai a saka shi a fim. Da wacce manufa ya shigo? Oho! Sai kawai a jefa shi ciki sai kuma wata tsiya ta faru a rasa yadda za’ayi. Ya kamata a je a zauna da iyayensu tare da kafa musu hujjoji kafin a yarda da shigowarsu. Wannan zai sa su su san cewar ba fa kara-zube suke ba.
Ya kamata gwamnati ta tabbatar da rajistar da kungiyoyin masu wasan fim domin lura da irin halayyarsu yadda da matsala ta samu za’a dakatar ko korar dan wasa.
Ya kamata a samu kamfanoni domin zabo ‘yan wasa. Hakan zai kara nuna amfanin rajistar ‘yan wasan da kuma kara daukar kansu a masayin wani jinsin mutane mai amfani da muhimmanci a cikin al’umma.
‘Yan jaridu su dage wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin bin tsarin addini da al’ada a cikin finafinan mu.
Domin tabbatar da da’a ya kamata a duba dukkan bangarorin yin fim misali yadda a ke wakokin cikin finafinan.
Jama’a masu kallo su rinka takawa duk wani fim da bai dace ba burki musamman a gidajensu. Su kuma rika fadawa mutane ta yadda hakan zai rage kasuwar shi wannan fim.
Ina fatan Allah Ya kare faruwar makamancin wannan abu, Allah Ya tsarkake dukkan ‘yan wasanmu domin samun fadakarwa wacce ta kamacemu da kuma daukakar wannan industri nake kuma fatan za’a gafartawa juna da nemawa wadanda suka yi wannan abu addu’ar neman gafara da shiriya.

Thursday, August 7, 2008

Is This Love or What?

Is this Love?
Today there are mixed reactions as to love between different set of people. People are approached and confronted by the opposite sex that they want to have an association whose form cannot be explained. With the advent of cell phone and internet it is realized that women/girls for instance communicate easily with men forwarding their requests for one relationship to another and vice versa. Many will believe with me that a lot of people have this experience. Please my readers, I will tell you my experience on how I was approached by these types of ladies. But what baffles me is, is it love they give and demand same in return? I do not know but may be we will find out together.

Before I share my experience with you I have found something as a background. What is love? What are the bases for love? Then what causes love?

Love
Deep affection or fondness

Basis of love
1. Without acquaintance and understanding, love does not take form, as man does not love one with whom he is not acquainted. For this reason he does not love a lifeless thing rather he can love one who has got life and understanding. (1) Mind likes a thing congenial to nature. (2) Mind hates a thing opposed to nature. (3) Mind hates what is injurious and pains-giving. So love means attraction of mind to what is tasteful and pleasure giving. When it is strong and firm, then there is deep love.

2. The second basis is that when it comes after knowledge and acquaintance. It is divided into several divisions from the stand point of knowledge and five senses. Every sense is satisfied with that thing over which it has got power and influence. Eye is satisfied with beautiful things, ear is satisfied with sweet sounds and songs, nose is satisfied with sweet scent and smell, tongue is satisfied with delicious foods, hand is satisfied with smooth touch. The object for which each sense finds delight is dear to it. The sixth sense is intellect, light, heart, mind or soul. The inner eye is more powerful than the external eye and the mind’s eye is more powerful than the external eye. The beauty which can be perceived through intellect is more than that of eye sight.

3. He who loves himself loves another for himself. Every living being loves his life. That means man wants that he should live forever and that his qualities should gain perfection. Nobody wants his destruction and loss of his qualities.

Causes of Love
1. A man loves his life than his limbs, than his properties, children, relatives and friends. Man does not love these things only for them, but for the fact that they help towards his long life and attainment of perfection. Even after his death, he wants to live through his heirs.

2. Another cause is getting benefit. A man loves one from whom he gets benefit as he is a servant of benefits.

3. To love a thing for its quality and not for the thing itself is another cause. A good figure is loved for its beauty.

4. Acquaintance with beauty is another cause. The external eye appreciates external beauty. A woman is beautiful when all her organs are proportionally beautiful. When her organs are not such, she cannot be called beautiful even though her colour is white. This is called acquaintance with beauty. So to get acquainted with perfection is a cause for love.

5. Secret connection between a lover and his beloved is another cause of love. Many a time love is cemented between them not for their beauty but for the union of their souls. The Prophet (SAW) said: ‘Out of them, love grows among those who have got similarity of souls’
If these qualities are found in one person, love for him is increased manifold. Power of love increases in proportion to the increase of those qualities in a man. If these qualities find full perfection in a man, love gains perfection.

Tuesday, August 5, 2008

Sharhin KUDI NE!


Sunan Fim: KUDI ne!
Kamfani:R.K. Studio
Labari, Shiryawa, Tsarawa, da Umarni: DanAzumi Baba
Masu Fadakarwa: Usaini Sule Koki, Bashir Nayaya, Shehu Hassan Kano, Ahmad S. Nuhu, Abba El-Mustapha, Amina Garba, Hajara Usman, Saratu Gidado, Zuwaira Abdulsalam da Zainab Idris.

JIGO
Kudi kare Magana

LABARI
Fim din ya fara ne da nuno wadansu iyalai guda biyu wadanda basa jituwa da junansu, basa ga maciji. Wadannan mutane sune Sinu (Shehu Hassan) da matarsa Adama (Hajara Usman) a bangare daya sannan da Danjuma (Bashir Nayaya) da matarsa Asabe (Saratu Gidado).
Suna zaune ne a gidan wani attajiri Alhaji Siddiku (Usaini Sule) inda suke yin aikatau a gidansa. To amma kasancewar wannan rashin fahimtar da ke tsakaninsu ya sa Alhaji ya fara gajiya da sasantawa, don haka a karshe ya yanke hukuncin basu jari na Naira dubu Dari Biyar-Biyar su duka biyun don hada su da abinda zai raba zaman da suke wuri daya har yake zama fitina.
To amma duk da haka kusan bata sake zani ba domin Danjuma musamman bai hakura ba. Haka su ma matan.
Ana haka har dai iyali suka samu kuma kamar yadda aka saba gani shi Sinu ya samu ‘ya mace wato Wasila (Zainab Idris) shi kuma Danjuma ya samu Mustapha (Ahmad S. Nuhu). Aka shiga soyayya ba tare da sanin hadin da ke tsakanin iyayen nasu ba. Rannan Mustapha yaje zance wurin Wasila, Sinu ya tambaye shi mahaifansa, shi kuma ya fada masa cewar shi dan Alhaji Danjuma ne. Nan take ya gaya masa kada ya sake zuwa wurin ‘yarsa. To haka shima bayan ya fadawa mahaifansa suka yi fatali da maganar.
Wannan soyayya mai sarkakiya ta janyo kace-nace tsakanin gidaje biyun. Amma su yaran tuntuni sun tsunduma cikin kogin soyayyar dasuke ganin iyayensu ba zasu iya raba su ba. Iyayen dai sun raba su amma a banza.
Wasila dai ta fice ta bar gidansu kan raba ta da masoyinta.
Kashegari itama Maijidda (Zuwaira Abdulsalam) wacce take gidan Alhaji ta tsunduma cikin soyayya da Balarabe (Abba El-Mustapha) wato dan shi Alhajin (Usaini) inda itama wannan soyayya ta gamu da nakasu daga Hajiya Sadiya wato mahaifiyar shi Balarabe. Dalilinta shine shi an haife shi cikin kudi don haka ya wuce matsayinta. A wannan dalili Maijidda ta arce daga gidan inda ta bar masa takarda tare da kaset na sako mai ratsa jiki, na bayanin cewar bata san ita ba ‘yar gidan bace don haka yanzu ta fice kuma bata san inda zata ba.
Alhaji dai yayiwa Hajiya nasiha da ta daina raina mutane marasa shi domin a sanadiyar takurawa Maijidda da tayi har ta bar gidan, hakan yayi sanadiyar kade ta da mota da yayi yayin binta don dawo da ita. To wannan nasiha dai da shige ta sosai.
A daya bangaren dai rigima ta ci gaba da rincabewa tsakanin Alh. Sinu da Alhaji Danjuma inda har Alhaji ya kirawo su don sasantawa da kuma jan kunnensu kan alfahari da dukiya da suke yi. Ya nuna cewar ai ‘ya’yansu sun fi su sanin abinda ya kamata amma su sun dage da kara habaka gabarsu don haka ya nemi su shirya amma suka ki. Anan dai ya basu sati daya na su dawo masa da dukiyarsa tunda sun ki natsuwa kuma sun ki yarda da hada ‘ya’yansu aure. Jin maganar kudi tasa suka shiga taitayinsu inda a nan take suka natsu kuma suka sasanta.
An yarda da batun auren shi kuma Alhaji yace idan har bayan sati ba a yi auren ba to fa zasu dawo masa da kudinsa.
Kudi kare Magana. Tilas suka hakura.
Wannan shine labarin wannan fim na KUDI ne!

SHARHI
Kamar yadda aka san Danazumi Baba wajen kawo sababin salo haka a wannan fim ma ya kokarta duk da kudi kan sa mutum ya kaucewa wani matsayi nasa, kamar yadda kudi yasa makiya a wannan fim suka shirya.
Labari ne wanda ya nuna yadda za’a iya canzawa duk mai wani mummunan hali akalarsa ta amfani da kudi wanda Hausawa kan yi wa take da kare Magana.
Umarni, labari , hadin ma’aurata sauti da daukar hoto duk sunyi kyau.


SAKO
Fim din KUDI ne! yayi kokarin gyara wadansu dabi’u da halayyar mutane da kawo sako kamar haka:
Amfanin kwantar da kai maimaikon tinkaho da masu kudi kanyi musamman ga marasa shi.
Nuna cewar kudi ba sune mutunci ba.
Kudi ba hauka ba ne.
Ladabtar da musamman matasa kan wadansu wasannin misali wasan mace da namiji.
Amfani da kudi wajen gyaruwar wasu al’amura maimakon amfani dasu don lalata mutane.
Amfanin nasiha domin daidaita mu’amalar mutane.

MATSALOLI
Ko da yake na san cewar KUDI ne! suke haifar da kaucewa nuna al’adar Bahaushe a finafinan Hausa to amma ya kamata a rinka kwatanta wakilcin tsarin rayuwa ta Bahaushe. Akwai wakoki a wannan fim. Nasan zai yi wahala a rabu da rawa da waka a finafinan Hausa ko kuma za a dau lokaci to amma ya kamata a dinga canza abin ta dabara maimakon kwafowa gaba daya.
Wakar farko ta Kudi tana da ma’ana, amma yadda masu nishadantarwar suka yi shigarsu, akwai ‘yar matsala domin ba kayan turawa ne kawai ke nuna kudi ba.
Waka ta biyu kam ba don harshen Karin wakar da Hausa aka yi ba gaskiya da sai mutum yace fim din Indiya yake kallo. Kai su kansu Indiyawa idan suka gani zasu yi farin cikin samun magada a wata nahiya.
Ya kamata a rinka kula da wani abu. A duk lokacin da aka haifi jarumi ko jaruma a finafinan Hausa to shike nan iyayen su sun daina haihuwa. Ya kamata a rinka dan jona ‘ya’ya mana. Ai akwai bambanci tsakaninmu da wadansu kabilun.

Hafsah


Sharhi kan Fim din Hafsah

Cast
Ali Nuhu
Zainab Idris
Nura Husaini
Hawwa Ali Dodo
Tanimu Akawu

Story development
Ian Masters
Sani Mu’azu
Iliyasu kasimu
Iliyasu Ibrahim

Script Consultant
Ian Masters

Research
Chinwe Nnoham

Camera
Ishaya Garau
Ibrahim Achimota

Editor
Babakarami Jos

Music
Habeeb M.
Nazeefi

Playback singers
Murja M. Baba
Nasiru idi
Habbeb M.

Production Executives
Jonathan Curling
Sani Mu’azu

Producer/Director
Sani Mu’azu

Sponsors
Lenscope Media
BBC World Service Trust.

Location
Bauchi

Gabatarwa
A kwanakin baya ne Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano karkashin jagorancin Mal. Abubakar rabo da haramta sayar da kaset din hafsah a fadin jihar domin a cewarsu Hukumar bata wanke shi ba. A dalilin haka shi kuma shugaban MOPPAN kuma mai fim din Hafsah Mal. Sani Mu’azu ya garzaya kotu domin kalubalantar wannan matsayi na Hukumar. A hirar da akayi da Mal. Mua’zu a jaridar Daily Trust ta ranar 15 ga watan Maris 2008, ya nuna ai tunda an wanke fim din sa a Abuja baya bukatar wata Jiha ta wanke shi. Sannan shi kansa Mal. Rabo ya yabi fim din a wani shiri na gidan rediyo, inji Mal. Mu’azu amma daga baya aka haramta fim ba.
Haka kuma ana cikin wannan sai ga wasu takardu da aka raba a masallatan Juma’a a birin Kano sun bayyana rashin jin dadinsu da irin wadannan finafinai ciki harda Fim din Sister da Hafsah wadanda babu komai a cikinsu sai bata tarbiyya. Wannan takarda dai mai taken “Asirinku ya tonu ‘Yan Kwagilar yahudawa” ta fito ne daga wata kungiya mai suna Islamic Values Protection Forum (I.V.P.F.) (Kungiyar Bada Kariya Ga Tarbiyar Musulunci).
A takaice wannan fim na Hafsah ya tayar da kura a lokacin da Hukuma ke kokarin tsarkake harkar finafinai musamman a Jihar kano. To amma me fim din ya kunsa? Shin su masu daukar nauyin sa sun yi domin fadakarwa ne ko kuma domin watsa tarbiyyar ‘ya’yan Musulmi Hausawa aka yi shi kamar yadda waccan kungiya tace?

Labari
Hafsah (Zainab Idris) wata yarinya ce wadda a farkon wannan fim aka nuno ta na cin gudu biye da ita wadansu samari ne wadanda sunyi kama da ‘yan daba. A gefen titi ta ci karo da wasu rumfuna na yayin kara inda ta fada daya daga ciki kamar ranta zai fita ba tare da sun ga inda ta shiga ba. Ashe wadannan rumfuna na wadansu mata ne, musakai da suke fita yawon bara. Don haka ta zauna a wurinsu duk da matsayinsu. Ta tashi daga barci sai taji suna wakar barar da suke yi idan sun fita don haka ita ma ta rinka bin wakar. Su da kansu abin ya burge su saboda zakin muryarta. Dalilin haka suka fara fita da ita yawon bara a kan tituna.
A bangare daya kuwa wasu matasa ne masu sana’ar kade-kade musamman tallace-tallace ga kamfanoni da bankuna suke cikin tsakar gwajin wakokin karkashin jagorancin Faisal (Ali Nuhu) da Linda (Hauwa Ali Dodo). Sun shiga tsaka mai wuya saboda rashin samun jigo da muryar da ta dace domin burge mabukatan wake-waken. Har ta kai ubangidansu (Tanimu Akawo) ya fara gajiya da rashin ci gaban da suke samu don haka ya basu lokaci ko su gyara ko kuma su san inda dare yayi musu.
Faisal da ‘yan tawagarsa sun fara neman mafita, don komai ya tsaya cik. Sun fara tunanin hanyar da zasu kama. Suna cikin wannan hali kwatsam sai Faisal da Linda suka ci karo da su Hafsah suna bara a kan titi, don haka Faisal ya fadawa Linda cewar waccan muryar tana da dadi. Suka kira su Hafsah suka basu sadakar N500. daga baya suka bi sawunsu suka nemi cewar idan suka yi amfani da muryar Hafsah zata iya zama wata tauraruwa. Kande da Hafsah basu yarda da binsu ba. Duk da haka faisal ya bata katinsa mai dauke da adireshinsa ko da zata nemi wani taimako.
Suna barin wurinsu Hafsah sai ga gungun ‘yan dabar nan karkashin jagorancin Jangwada (Nura Hussaini) sun dira a makwancin su Kande inda suka bankawa rumfunansu wuta. Lokacin da wutar da kusa cinye kayan rumfunan sai Hafsah ta tuna da katin da faisal ya bata ko da zata bukaci taimako. Nan da nan ta tono katin. Ta nemi waya ta buga masa. Ya zo ya same su ruwan sama yana faman dukansu. A haka ya nema musu matsuguni. Ita kuma ya kaita wurin da suke gwajin wakokinsu. Nan ya bukace tada ta rera irin wakar da suke yi idan sunje yawon bara. Ta rera wakar wacce ta baiwa duk ‘yan kungiyar su faisal sha’awa saboda zakin muryarta.
Linda ta je ta nuna mata daki mai kyau a matsayin wurin da zata zauna. Linda ta fara tambayarta inda ta fito, to amma Hafsah ta nuna wani irin rashin jin dadi. Ana haka sai ga Faisal da wasu kaya da ya sayo mata, amma Linda tayi kyashin wannan kaya. Bisa yarda da Faisal yayi na biyawa su Kande kudin haya, Hafsah ta yarda zata sanya kayan.
Bayan ta shiga wurin wakarsu suna gwaji sai ta ji rashin dadin irin salon wakar da suke yi don haka ta bukaci ayi wakar gargajiya. Faisal ya fada mata cewar su basa wakokin gargajiya. Kawai sai ta kaure da wata waka ta gargajiya mai suna Jalla-ku-jalla inda hakan ya burge kowa a wurin.
Sun kai wasu Kande ziyara. Faisal ya nemi jin asalinta domin bata yi kama da suba. Ta nemi kawai yayi shiru. Sun koma wajen wake-wakensu don koya mata rawar zamani ita kuma ta nuna ita fa ba zata iya ba. Linda ta dan nuna mata irin rawar da suke so. Ta dai nuna ita ba zata iya ba. Linda ta furta cewar dama ita Hafsah ‘yar kauye ce, don haka ba zata iya komai ba. Ai kuwa nan Hafsah ta zuciya, ta tambayi makadin ko yayi zaman kauye, ya amsa cewar eh. Ta ce to ya buga mata kidan kalangu. Nan ta tsuge da wata irin rawa mai ban sha’awa. Abin ya ba kowa sha’awa a wurin. Tana cikin rawar sai ga ubangidan su faisal (Tanimu Akawu) a tsaye da wasu ‘yan sanda. Ya ce ai ba don abinda ya taras ba da yau zai sallamesu. Don haka ya bukaci ‘yan sandan da su koma.
A dalilin ganin irin soyayya da take neman shiga tsakanin Hafsah da faisal, Linda ta fara nuna kishi.
Anan cikin gwajin waka sai ga wani ya shigo cewar ga wata kuturwa tana neman Hafsah. Linda ta bayyana cewar bai kamata a rinka yawan zuwa kiran Hafsah ba balle kuma kutare. Faisal ya bukaci Hafsah ta dakatar da zuwa wurinta da su ke yi. Nan ta fara tattare kayanta saboda rashin jin dadin abinda ke faruwa. Dole Faisal ya hakura.
Wani lokaci Hafsah ta je domin ganin Kande wacce bata da lafiya har Linda ta bita. Linda ta samu daya daga cikin abokan zaman Kande har ta jiyo sirrin Hafsah. Sakamakon haka har aka nuno Linda ta ziyarci Jangwada.
Ana haka har faisal ya sayo wa Hafsah abin wuya mai kyau amma tace ita bata bukata domin akwai abinda ke damunta.
Bayan nan ta samu su faisal ta nemi izinin fita kamar yadda ta saba. Sun nuna mata su fa sun gaji da yawan fitar ta domin yana shafar sana’arsu.
Tafiya tayi tafiya, soyayyar Hafsah ta shiga zuciyar Faisal. Ya nuna mata shi bai taba ganin mace irinta ba. Amma ta dakatar da shi cewar ita ba son wata hulda da wani namiji, kawai dai suyi huldarsu ta waka.
Ita kuma Linda ta fara janyo Hafsah a jiki don jin wasu abubuwa inda Hafsah ta nuna mata ta daina shiga harkokinta. Nan Linda ta ci mata mutunci, ta kuma fada mata sai ta fallasa ta.
Saboda shiga halin kaka-ni-kayi da faisal yayi, ya shiga wani hali, hankalinsa ya dugunzuma, ya ware a cikin dakin kade-kadensu yayi ta tikar rawa. Yaransa suka zo suka zuba masa ido. A karshe sauran kiris ya fadi, Hafsah ta je a guje domin tallafarsa amma ya ce kawai ta kyale shi domin ita maciyiyar amana ce. Anan tace ita su fita daga harkarta. Nan tayi fushi ta kama hanyar fita daga wurin sai ga Ubangidansu ya dawo da ita inda ya nuna ai ita ce ta ceto su a wannan sana’a. Ya nemi a bata hakuri kan ci mata mutuncin da akayi. Tilas Faisal ya bata hakuri. To amma nan Linda ta fizgo abin magana ta kwalla kiran Jangwada. Nan ya fito da ihun yau karyar warai-warai ta kare. Ya fadi cewar Hafsah matarsa ce bai kuma turo ta don tayi rawa da waka ba. A dalilin haka ubangidan nasu ya bukaci Faisal daya binciko abinda yake faruwa domin shi fa ya gaji da wannan wasan kwaikwayo da ke faruwa.
Anan Hafsah ta nemi Jangwada ya sauwake mata. Nan ya bukaci naira dubu ashirin idan tana son ya sake ta. Ta yarda to amma ya ja kunnenta da na Faisal in ba haka ba zai tona wani asiri nata. Bayan nan Linda ta fallasa cewar ai Hafsah tana dauke da cutar kanjamau. Take faisal yace Linda ta bar wurin kada ta kara dawowa. Ita kuma ta fada masa cikin fushi cewar da ta zauna da mai cutar kanjamau gara tirela ta buge ta. Nan Jangawade yace shi dama Faisal bai san abinda ke faruwa ba?
Faisal ya tambayi Hafsah ko da gaske ne ta da wannan cutar. Ta fusata tace eh tana da ita kuma tana da aure, sai me?
Allah Ya yi wa Kande rasuwa. Hafsah tayi juyayin rasuwar Kande wacce ta rike ta a cikin wannan mawuyacin hali.
Faisal ya tambayeta abinda take shirin yi, tace ita Lagos zata koma. Yake fada mata shi ya rasa kanta musamman kan wannan cuta ta ta. Ta fada masa cewar tana nan a Hafsar daya santa kuma tana da kanjamau. Ya nace kan ta fada masa tarihinta.
Ta fara bayyana yadda ta hadu da Jangwada wanda wani matashi ne mai farin jini a kauyensu, ga shi a lokacin yana da irin mashi wanda yake wasa da shi a kauyen, har a kan kewayeshi ana kallo. Wata rana ya je gidansu Hafsah yace yana sonta. Ya kuma kawo maganar aure ita kuma ta yarda.
Bayan sun yi aure sun koma birni da zama. A haka ta samu juna biyu. Saboda laulayin cikin ta nemi zuwa asibiti, amma surukarta ta rinka bata maganin gargajiya maimakon zuwa asibitin.
A nasa bangaren, Jangwada ya rinka fama da wani matsanancin zazzabi. Shi ma dai ya rinka shan maganin gargajiya har ma wani lokaci ya kan sami sauki.
Ita kuma Hafsah ta shiga nauyayyiyar nakuda wacce ta sha wahala. Tilas dai aka kaita asibiti amma a dalilin wahalar da ta sha har aka rasa abinda ta haifa. A cikin irin gwaje-gwajen da aka yi wa hafsah a asibitin har aka yi rashin sa’a aka sameta da cutar kanjamau.
A haka fa kowa ya tsangwameta wanda hakan ya tilasta mata komawa cikin birni. To amma Jangwada ya hana ta sakat don kuwa yayi ta turo mata ‘yan banga don cuzguna mata. Dalilin haka ta samu su Kande wadda ta rike ta. A nan ta gane cewar matsalarsu iri daya ce domin su ma an tsangwame su saboda cutar kuturta.
Ta samu ilimi daga likitar da ke kula da ita kan yadda zata iya tafiyar da rayuwarta cikin kwanciyar hankali. Aka dora ta akan magunguna wanda wannan ne dalilin yawan neman izinin da take yi daga wurin su Faisal.
Faisal yayi mamakin labarinta don haka ya nuna cewar lallai tana da bukatar kulawa. Ya fada mata cewar matsalar sa shine ya guji ‘yan uwansa ne saboda ya samu ci gaba a sana’arsa ta wake-wake. To amma har yanzu yana kewarsu. Ta ba shi shawarar ya je ya sasanta da iyayensa da ‘yan uwansa. To amma sai mamaki ya kamata domin ga shi tana bashi shawara amma ai ita ma babu daidaito a tsakaninta da danginta. Sai ya nuna mata ai su suka guje ta. Shine ta nuna ba laifinsu ba ne, a’a jahilcin sanin cutar kanjamau ne ya kawo haka.
A bisa shawarwarin da suka yi, Hafsah ta je gida domin samun daidaito da dangin nata. Mahaifiyarta tayi mamakin ganinta. Ta kuma fadawa Hafsah cewar ai Jangwada ya lalace, ya bushe. A dalilin haka Hafsah ta ziyarce shi amma mahaifiyarsa ta kama zaginta cewar ta zo don karasa shi bayan ita ta saka masa cutar kanjamau. Nan ya nuna ai ba laifinta ba ne, laifinsa ne. Hafsah tace ya zai ce laifinsa ne?
Nan ya nemi gafararta domin halin da suka shiga shi ya janyo domin shi ya dauko cutar a cikin harkokinsa da yake yi da matan banza a birni. To amma tunanin babu cutar da bata da magani ya sa ya sakankance ya hau shan maganin gargajiya. Ya dai bata hakuri kan lalata rayuwarta. Ya kuma yi nadamar shiga wannan hali, ya fada mata cewar dalilin kai mata farmaki shine domin bakin cikin halin da suka shiga. Ta dai yafe masa amma ta bashi shawarar ya rinka shan magani, ta kuma karfafa masa gwiwar ci gaba da rayuwa.
Anan ya fada mata tarihin yadda ya sameta kafin suyi aure. Domin wata rana yaji muryarta tana waka yayi sha’awar muryarta ta wadda hakan ya sa ya je neman aurenta. Ya kuma bayyana mata cewar kudin daya bukata daga gareta yayi ne don sayen maganin da zai sha.
A karshe dai ya bayyana cewar ya sake ta. Mahaifiyarsa ta nuna ai tunda Hafsah ta nemi su sasanta ai ya kamata ya hakura. Ya dai tsaya a wannan matsayi nasa.
Faisal ya nuna damuwarsa kan dalilin nacewar da Hafsah tayi wa Jangwada. Tace ai ita don tana son taimaka masa ne. Nan faisal ya fada mata cewar shi fa son ta yake yi. Shin akwai yiwuwar su iya aure a tsakaninsu, a matsayinsa na wanda bashi da wannan cuta? Domin hakan na damun mutane da yawa. Take fada masa cewar a asibiti an taba fada mata cewar za’a iya yin aure da mai cutar da maras ita har ma su haihu ba tare da dan da zasu Haifa ya kamu da cutar ba. Ya ce to shi ko zai so yaje asibitin domin karin bayani don har ila yau ya san matsayinsa. Ta ce ta yarda amma tana son ta taimakawa Jangwada.
Hafsah dai ta zama kasaitacciyar mawakiya inda take wakar ‘HIV ba zai kashen ba’ inda take bayyana halin da ta shiga da kuma tabbacin rayuwa da cutar cikin kwanciyar hakali. Itama Linda ta shiga wakar tana karfafawa hafsah cewar kada ta damu.
Shi kuma faisal a wani baiti cikin wakar da sigar wakar rap yake cewar:
‘Just imagine how you’ll feel, if you are down and helpless and still got discriminated by your very own, read between the lines, it ain’t easy surviving through the rough, tough times, Hafsah the extraordinary how ever though situations, you never gave up, kept holding on, still keeping your head up, how many more can survive all you’ve been through. The cloudy days are over now. The sun is shining, yes, I’m signing out. I know your story gonna inspire a lot.’
Can kuma wata muryar a cikin wakar ta ke cewar:
‘despite your status you could still give hope to the hopeless. Hafsah lets keep hope alive’.
Wakar ta ba duk ‘yan kallonsu sha’awa ciki har da Jangwada wanda ya sara mata.
Nan fim din ya k are.

Darasi
Babban darasin wannan fim na Hafsah shine nuna rashin wariya ko kyamatar mutane wadanda suke dauke da wata cuta misali kanjamau da kuturta.
Amfanin fahimtar kasancewar wasu cututtuka.
Amfanin dogaro da kai.

Sharhi
Wannan fim yana shan suka musamman ga wadanda suke da kishin al’adar bahaushe da addinin Musulunci. Ina ganin masu fim dim ba su yi la’akari da ko daya daga bangaren addini ko al’ada ba illa dai kaunar kidan gargajiya da Hafsah take da shi.
Idan aka dauke rayuwar mutanen kauyen su Hafsah da kuma abokan zamanta a lokacin da su jangwada suka biyo ta babu inda aka nuna akwai wata al’ada ta Bahaushe ko kuma aka baiwa suturar bahaushe muhimmanci. Watakila za’a iya basu uzurin fim ne na matasa kuma musamman mawaka domin gaba daya a kananan kaya suke. Gajeruwan wanduna da guntayen riguna da duguzuzun suma ga samarin fim din da kuma matsattsun kaya ga matan musamman Linda wacce dama ita da alama ba Bahaushiya ko Musulma b ace a fim din ya nuna halin matasa na yau. Linda tafi Hafsah shigar rashin mutunci domin babu a inda aka nuno ta da shiga ta kamala. Ina jin wannan shine dalilin dirar mikiya da yawancin masu kallo suke yi ga fim din. Amma ita Hafsah kam da dan dama-dama tun da ta shiga wasu halaye da yanayin wurin ya kan sa ta canza ta sa doguwar siket.
Masu yin fim din sun dau sana’ar wake-wake ne kila saboda jan hankalin matasa kan sakon da suke son isarwa. Dukkan ‘yan kungiyar sun nuna burgewa wajen kwaikwayon yadda mawakan zamani su ke. Ta bangaren rawa lallai dukkan su sun cashe musamman irin rawar da Hafsah ta rinka takawa. Muryar da aka yi amfani da ita a wake-waken ta yi zaki kwarai, kuma su kansu wadanda suka bi wakar musamman Hafsah ta burge, kamar ita take rerawa.
Dole a jinjinawa Faisal (Ali Nuhu) bisa irin rawar da ya dinga takawa, da cashiya wacce ta nuna kowanne mataki aka bashi zai iya dauka a fim. Haka ita ma Linda (Hauwa Ali Dodo) wacce ta taka matakin fitowa a wani rol mai wahala, domin duk wanda ya taka shi tabbas zai gamu da fushin mutane da yawa. Uwa uba Hafsah ta yi kokari na fitowa a mai kanjamau, ga kuma zaman da tayi da kowanne fanni na rayuwa a fim din. Gata da kokarin son kidan al’ada kasancewar ta ‘yar kauye. Shi ma Jangwada (Nura) ya gwada irin basirar da Allah Ya bashi da iya zama komai ciki har da zama dan daba. Su ma kungiyar su Kande sun nuna irin yadda ake zama a wannan matsayi na musakai.
Labarin ya tafi daidai da jigon fim din duk kuwa da walankeluwa da aka rinka yi da hankalin masu kallo ta yadda da wuya a gane abinda zai faru a gaba. Kusan ganin yanayin jikin Jangwada babu wanda zai zaci za’a samu cutar kanjamau a jikinsa kila a nan ana son nuna wani sakon da masu irin wannan fim kan nuna na cewar ba’a gane mai cutar kanjamau ta fuska.
Jigon fim din ya dace domin kara wayar da kan jama’a tattare da kyamar wani jinsi na mutane. Ya kuma fadakar game da yadda matasa ya kamata su rinka hulda idan sun fita neman kudi musamman a birane. Ya nuna cewar za’a iya rayuwa ko da an kamu da wannan cuta, kuma kalmomin da aka ambata a cikin wakar karshe mai cewar ‘despite your status you could still give hope to the hopeless. Hafsah lets keep hope alive’ ta karfafa gwiwa kan kowanne matsayi da Allah Ya sa mutum.
Ai ba sai an fada ba, fim din ya dauku matuka, kyamar rangadadau. Location din da aka dau fim din a garin Bauchi ya burge saboda yanayi da kuma amfani da wurin gwajin kade-kaden. Jarumai sun bi umarnin darakta sau da kafa. Kana ya nishadantar da mai kallo, musamman matasa.

Matsaloli
Kamar yadda na fada a baya, babbar matsalar fim din Hafsah shine rashin baiwa al’ada ko addini muhimmanci.
Babu inda aka nuna Faisal ya je wurin mutanensa domin neman gafararsu.
Hafsah ta fadawa Faisal cewar za’a iya yin aure tsakanin mai dauke da cutar kanjamau da wanda bashi da ita, me yasa ba’a yi cikakken bayani ba domin kila hakan zai kara nuna kauna ko kaucewa tsana ga masu dauke da cutar.
Kayan da jangwada ya rinka sanyawa kamar ya dade yana sawa, misali tun yana kauye har kuma karshen fim din. Me ya faru?
Me yasa ba’a nuna yadda za’a guji kamuwa da cutar kanjamau ba? Domin babu wani darasi da zai nuna Jangwada ya shiga wani hali, kila ma a nuna ya mutu domin gudun kamuwa maimakon har azo kan tsangwamar mai dauke da ita illa dai yanayin daya shiga, mai kowacce irin cuta ma zai iya shiga.
Me yasa aka sanyawa sunan fim din Hafsah? Domin anyi kukan cewar sunan yana da girma a addinin Musulunci. Kamata yayi a sa suna kamar ‘Tsangwama’ ‘Fadakarwa’ ko makamancin haka.

Rayuwa

Ita rayuwa ta danganta daga mutum zuwa mutum. A hankali mutum kan shiga wadansu halaye da canza rayuwarsa har kuma ya san yadda zai rinka mu'amala da sauran jama'a. Don haka ina ganin yana da kyau daga lokaci zuwa lokaci na rinka gutsuro wadansu al'amura na rayuwa ta yadda na fahimce su.