Tuesday, February 22, 2011

JARUMAN FINAFINAN HAUSA: UMAR GOMBE

JARUMAN FINAFINAN HAUSA: UMAR GOMBE
Umar Gombe yana cikin matasa da ake damawa da su a finafinan Hausa na wannan zamani. Yadda yake fitowa a finafinai musamman a matsayin matashi a duk matsayin da aka bashi da yadda yake fitar da iya kokarinsa don ganin ya baiwa maras da kunya na ga ya dace na dan tsakuro tarihinsa da yawan finafinan da ya fito.
Asalin sa dai dan Gombe ne wanda aka haifa shekaru 23 da suka wuce.
MATSAYIN KARATU
Umar yayi makarantar renon yara (nursery), Firamare da Sakandare a Gombe lokacin tana hade da Jihar Bauchi daga 1986 – 1998.Yaci gaba da karatun inda ya samu difloma a bangaren sarrafa komputa a New World Computers Professional Institute wacce ke da rajista da Jami’ar Lagos a 1999. Ya kara yin difloma a fannin shugabanci wato Public Adminstration daga jami’ar Bayero, Kano daga 1999 – 2003.Yanzu kuma yana karatu a Jami’ar Ambrose Alli inda yake koyon aikin adana kudi.
JARUMIN FINAFINAI
Ya fara fitowa ne a shekarar 2001 a wani fim da Marigayi Tijjani Ibrahim ya bayar da umarni mai suna Shaida wanda kamfanin AL-NASEED PRODUCTION suka shirya. Yarinka fitowa a finafinan da kamfanin Fasaha Films suka shirya daga baya ya koma Brightstar Entertainment, FKD Productions da kuma wasu kamfanoni da ya yiwa finafinai. Yayi fice a finafinan ISI Films inda suke tare da Ishaq Sidi Ishaq.

Umar yana daya daga cikin matasa masu ladabi da biyayya duk da kasancewarsa matashi kuma wanda yake da asali daga babban gida. Mutum ne mai hazaka da girmama jama’a. Harkokin fim basu hanashi kokarin yin karatun zamani ba ta yadda zai iya ci gaba da kawo sauyi.
Hakika yanayin fim dinsa yana burge masu kallo musammman idan ana son nuna matashi. Wajen sanya sutura ba’a barshi a baya ba domin duk kayan day a sanya a fim suna burge masu kallo.

FINAFINAI
Jarumin ya fito a finafinai sama da 100 wadanda suka hada da:
A dream forever (an english film)
Akurkin Kauna
Al'ameen
Albashi
Ambaliya
Attajira
Babbar harka
Bakar Ashana
Biko
Bin Iyaye
Budurwa
Daidaito
Da'ira
Faifai
Farin Wata
Fasbir
Fice
Fida
Fifita
Fika
Gadali
Gwanaye
Gwamna
Harsashi 3
Haske
Halimatus Sadiyya
Hidima
Igiyar So
Iko
Indararo
Intaha
Irada
Iyaye
Jami'a
Jari
Jarumai 2
Jarida 2
Jawabi
Kadara
Kamilu
Kalangu
Kalle Ni
Kalma
Kampala
Kasafi
Katari
Kasarmu
Kirtani
Kusurwar Danga
Kewayya
Kwalla
Labbati
Lada
Langa
Likkafa
Lissafi
Maimunatu
Maliya
Masoya
Naira
Nauyi
Nakiya
Noor
Qasadi
Qumaji
Rairayi
Rarrashi
Reshe
Rikoh
Rumbu
Rumfa
Sallama
Sa'in sa
Sama
Samari
Sankace
Sansani
Sauyin Yanayi
Sheeka
Shinkafa Da Miya
Takunkumi
Tagwaye
Tarairaya
Takbair
Talle
Tofi
Tutar So
Tutiya
Umarni
Wa'azi
Wakilchi
Wasali
Wasila Enlish Version
Yanka
Zabi Sonka
Zinariya
419 (Damfara)

No comments: