Daga
Yusuf Ubale Ajingi
Sunan Fim Rikoh
Kamfani Dutsen Gima Movie Planet/FKD Production
Shiryawa Bashir Muhammed Dutsen Gima
Labari Bashir Muhammed da Ali Ibrahim Khalil
Umarni Ali Nuhu
Shekara 2005
Masu Fadakarwa Ali Nuhu, Jibrin S. Fagge, Saima Mohd,Jamila Haruna, Hajara Usman, Kabiru Nakwango, Shehu Hassan Kano, Bashir Nayaya dss.
Labari
Wannan fim yana tafe da babban sako na nuna yadda riko yake da illa har ya kai mutum ga yin aika-aika.
Labarin wani attajiri d’an kasuwa ne mai suna Alhaji Kabiru (Kabiru Nakwango) wanda yake da k’ok’arin sauk’ak’awa jama’a wajen tabbatar da sayar musu da kaya akan farashi kamar yadda kamfani yake bashi. Hakan da yake yi bai yiwa d’an uwansa kuma abokin huld’ar kasuwancinsa Alhaji Hassan (Shehu Hassan Kano) d’ad’i ba kuma yana ganin wannan zai iya durk’usar da harkokin nasa tun da jama’a zasu bar wurinsa su koma wurin shi Alhaji Kabiru. Yayi k’ok’arin ganin ya jawo hankalinsa kan illar da yake yi masa, shi kuma ya dage kan wannan hali na taimakawa. Matar Alhaji Hassan, Hajiya A’isha (Jamila Haruna) kullum k’ok’arin da take shine na jan hankalin mijinta don daina wannan gaba daya d’aukarwa kansa. A taik’ace shi dai bai ja da baya ba kan ganin karshen abin ba har kuma yake fada mata cewar zai iya daukar kowanne mataki don ganin ya sami galaba.
Akwai lokacin da suka hadu da Alhaji Kabiru inda har yake nuna masa kiri-kiri cewar ba ruwansa dashi tunda niyyarsa yaga ya raba shi da harkokinsa. Alhaji kabiru yayi masa nasiha amma ya tsaya daram kan hakilon da yake yi a inda har yayi barazanar cewar zai iya hallaka shi kan wannan. Alhaji kabiru yayi mamakin wannan lafazi na kisa.
Kwatsam rannan Alhaji Kabiru yana dakinsa yana barci wasu karti suka danne shi suka kashe.
Saboda furucin da yayi na kashe Alhaji kabiru, ai ba wata tababa matarsa Hajiya Hajara (Hajara usman) tare da dansa Abba (Ali Nuhu) suka kai Alhaji Shehu wurin ‘yansanda inda aka fara gana masa azaba domin amsa tuhumar da ake yi masa. Shi kuma ya tsaya tsayin daka cewar ba shi da ruwa wajen wannan kisa.
A wani bangaren kuma kafin rasuwar Alhaji Kabiru saboda kauna da jin dadin kammala karatun dansa Abba, yayi masa albishir da saya masa mota irin wacce yake so. Don haka ya tafi wurin Alhaji Sa’idu (Jibrin S. Fagge) tunda yana sayar da motoci domin ya zaba. Aka gaya masa su zo da mahaifinsa domin zaba. To amma a dalilin tafiya da mahaifin nasa yayi sai mahaifiyarsa tazo.
Suna zuwa sai Hajiya Hajara ta gane shi har take tambayar sa cewa dama yana Kano? Anan dai ta nuna Abba a matsayin danta.
Ba a dade ba aka yiwa Alhaji Kabiru wannan kisan gilla. A bayan nan ne Alhaji Sa’idu ya rika ziyarta Hajiya har yana kyautata mata dai dai gwargwado kuma dama garinsu daya wato Gombe wadda wannan tasa ake tunanin ko ‘yan uwa ne. Ana haka har dai ya nuna maitarsa a fili na son auren ita Hajiya Hajara. Ita kuma ta nuna masa cewar ai ta riga ta yiwa wani aminin marigayin mijinta alkawarin auren sa. Shi kuwa Alhaji sa’idu ya dage kan ko ta hali ka-ka sai ya aureta kuma zai iya aikata komai kan ganin hakan. Ashe da walakin wai goro a miya, ya taba nemanta da aure tun suna matasa amma aka hana shi saboda kamar yadda yace bashi da kudi. Ba a dade da wannan batu ba manemin Hajiya shima ya mutu.
Ana ta jimamin kisan da aka yiwa Alhaji Kabiru sai wani mutum wanda yake abokin Alhaji Sa’idu ne wato Alhaji Ya’u (Bashir Nayaya) ya tseguntawa Abba cewar ga wanda ya kashe mahaifinsa. Nan da nan suka dunguma tare da ‘yan sanda aka kama shi. Duk daya musanta zargin daga baya ya amince kana kuma ya bayyana yadda ya sha fama da masifar son Hajara a can Gombe lokacin suna matasa amma saboda rashin kudi aka hana shi. Shi kuma saboda zuciya nan ya tattara nasa ya nasa ya cilla Ikko da niyyar shi ma sai ya nemo kudin da zai iya aurenta. Ya je kuma ya samo kudin. Sai dai kash! Yana dawowa aka fada masa ai tayi aure kuma suna Kano. Nan yayi niyyar nemota koda zata kai ga kashe wanda ya aureta ne. Wannan shi ya rike a zuciyarsa har bayan shekaru masu yawa ya aiwatar da nufinsa.
Wannan shine labarin wannan fim na Rikoh.
Sharhi
Wannan fim shine na farko da kamfanin Dutsen Gima Movie Planet tare da jagorancin FKD Production ya shirya.
Labarin fim din yana da karfi da sarkakiya tare kuma da jan hankalin mai kallo musamman kan wanda yake da alhakin kashe Alhaji Kabiru domin ganin furucin da Alhaji Hassan ya sha yi kan abubuwan dake tsakanin su. Wannan zai sa mai kallo ya tabbatar cewar lallai shi ya sa aka kashe shi.
Duk da cewar akwai soyayya a cikin wannan fim amma jigon labarin yana nuna yadda riko a zuci kan haddasa aikata wata aika-aika tare kuma da nuna yadda gaba kan kullu kan neman abin duniya musamman harkoki irin na kasuwanci.
Fadakarwa/Burgewa
Masu shirya wannan fim sun yi kokari tunda wannan shine na farko da suka saki. ‘Yan wasa tare da uwa-uba mai bayar da umarni suma sunyi kokari. Kadan daga cikin abubuwan daya kunsa sun hada da:
Amfanin kyautatawa al’umma da iyali.
Illar dagewa wajen aurar da mace ga mai kudi kawai duk daya kamata ace manemin yana da madogara domin kula da matar.
Nuna shawara ta gari daga mace don kwantar da hankalin miji don kada ya aikata aikin dana-sani.
Duk da kusancin abokantaka bai kamata a rika boye mugun sirri ba musammnan idan laifi aka aikata.
Nuna cewar baki shi kan yanka wuya, ma’ana mugun furuci bashi da amfani.
Illar rikon mutum a zuci da irin bala’in da yake jawowa mai irin wannan hali.
Kurakurai/Shawarwari
Duk da kokarin da akayi wajen yin wannan fim akwai ‘yan matsaloli da ba za’a rasa ba da kuma ‘yan shawarwari domin gyaran gaba.
Babu wani sakamako da aka yiwa Alhaji Kabiru a fim din kan irin kyautatawarsa wanda hakan zai karawa masu irin wannan hali azama. Kawai sakamakonsa shine kisan da aka yi masa.
Ya kamata ace bai dau maganar da Alhaji Hassan da wasa ba. Ya kamata ace ya dau mataki ko da ta hanyar tsaron kansa ne ko fadawa hukuma.
Duk da kamun da aka yiwa Alhaji Hassan to amma ba’a san makomarsa ba tunda zai iya yafewa ko kuma ya dau wani mataki musamman irin azabar daya sha a hannun’yan sanda (ko sai a kashi na biyu idan da akwai?)
Soyayyar Abba da Zainab (Saima Muhd) bata da wata dangantaka da fim din.
Haka zalika wakokin da aka saka an yine kawai domin nishadantarwa domin jan hankalin masu kallo tun da cashiya suke bukata.
Ya kamata ace matar Alhaji Hassan ta ja hankalinsa bayan an sallame shi daga wurin ‘yan sanda kan illar irin matsayinsa na gaba da kullatar mutum da kuma fadar Magana ba tare da ja ma bakinsa linzami ba wadda hakan zai kara fadakar da masu kallo. (Watakila sai a kashi na biyu)
Duk da kasancewar kalmar RIKO ta dace da labarin amma wajen rubutawar bai kamata a kara harafin ‘h’ ba. Amma ban san abinda malaman harshen Hausa zasu ce ba.Shawara ta anan shine a daure a rika tuntubar masana harshen domin tabbatar da yadda ake rubuta kalma.
Duk da kauna da Hajiya Hajara take yiwa mijinta sai gashi bayan sati biyu kacal da mutuwarsa an nuno ta tasa talabijin a gaba duk da a lokacin ana cikin alhinin wannan rashi.wadda a al’adar Bahaushe kusan hatta sauraren rediyo ko hayaniya ba a yi sai an dau tsawon lokaci.
Babu wani kokari da akayi wajen nemo masu kisan domin suma a hukuntasu. Kawai sun yi kisa sun kama gabansu sai dai idan za ayi hakan a kashi na biyu in kuma ba haka ba to an daurewa ‘yan ta’adda gindi kenan.
Ya kamata a ce an nuna kwarewa saboda ci gaban zamani wajen zakulo wadanda suka aikata kisan misali ta hanyar daukar hoton hannun masu laifin akan mayafi da filon Alhajin lokacin da suka kashe shi maimakon dogara da shaida ta baki wacce bata da inganci sosai.
Ina fatan za’a samu gyara kan irin wadanda abubuwa da ake samu a cikin finafinan mu.
No comments:
Post a Comment