Monday, August 11, 2008

SHARHIN FIM DIN FASSARA 1 & 2

SHARHIN FIM DIN FASSARA 1 & 2
Daga
Yusuf Ubale

Sunan Fim: Fassara
Kamfani: Al’umma Production
Daukar Nauyi: Gali Lawan Zango
Umarni: Ashiru Nagoma
Masu fadakarwa: Shehu Hassan, Kabiru Nakwango, Bashir Nayaya, Ali Nuhu, Ashiru Nagoma, Adamu A. Zango, Hafsa Shehu, Rukayya Umar, Aina’u Ade, Mansura Isah,Jamila Haruna dss.

‘Duniya susar jaki ce, yi mini nai maka. Kowaye a duniya idan yayi sai anyi masa. Duk mutumin daya tsallaka katangar wani ko ya tsugunna akan katangar wani yayi kashi to sai an ketara tasa ko an masa kashi shima. Idan kayi a katangar mutum kwaya daya, goma sai sun yi a taka.” Kabiru Nakwango a cikin fim din Fassara 2.
A wannan karon ina son zanyi sharhi ne akan fim guda daya amma kashi na daya dana biyu. Ban sani ba ko an yi sharhin na dayan to amma saboda sako da muhimmancin wannan fim tare kuma da samun cikakken bayani shine dalilin hadawa domin hasko irin hasken da wannan fim yake koyarwa.
Kashi na farko
Labarin ya fara ne da nuno wani Alhaji (Shehu Hassan) yana zaune da ‘yarsa Lubna (Hafsa Shehu) wacce mahaifiyarta ta rasu ta bari tare da uban da kuma yayanta Babangida (Ashiru Nagoma). To shi dai mahaifin nasu saboda dalilin da shi kadai ya sani ya ki sake wani auren bayan rasuwar ita mahaifiyar ‘ya’yan nasa. Ita Lubna ta girma yadda har ta isa aure amma saboda wani dalili da kuma hankoronsa na son ganin ta auri mai hannu da shuni yasa ya ajiyeta a gabansa duk da irin matsin lamba da yake samu daga surukansa (Kabiru Nakwango da Jamila Haruna) da suke ta hura masa wuta kan ganin ya aurar da ita domin barinta haka bai dace ba. Sun nuna masa tunda dai ga manemi ta samu ai kawai sai ayi. Amma shi ya tsaya tuburan cewar shi yaron da yake nemanta fa wato Nasir (Ali Nuhu) ba wani abu gare shi ba domin a wuri daya suke aiki yasan shi. Shi kawai sai ya samu wanda a ganinsa ya dace da ‘yarsa.
Kamar yadda koyarwa addinin Musulunci da al’adar Hausa take koyarwa zaman da yake shi da ‘yarsa yana da hadari. Wannan zama yasa ya kyasa irin yadda take musamman idan taci ado da irin kananan kayan nan na zamani. Ko da yaushe tana gilmawa ta gabansa, ta dafa musu abinci, kai a takaice suna zaune su kadai a gidan. A irin haka dai har akwai lokacin da ta fito zata shiga bayan gida shi kuma yana zaune a falo ya tambaye ta me zata yi. Ta fada masa, yace ai sai tayi amfani da na falon. Don haka tana shiga ya bita ciki inda abin da zai auku ya faru.
A sakamakon wannan mummunar saduwa da yayi da ‘yarsa ta shiga halin damuwa. Domin hakika ita ta tabbatar wannan abu bai dace ba. Sakamakon dai wannan haduwa juna biyu ya shiga wato ta samu ciki.
Shi kuma Nasir ya dage ganin lallai sai ya kara aure musamman Lubna wacce suka shaku duk da wulakancin da mahaifinta yake yi masa. Kuma hakika ya gamu da gumurzun matarsa wacce ta dorawa kanta bakin kishi. Duk da haka ya tsaya kan bakansa har dai shi uban Lubna ya aurar masa amma ba wai don yaso ba a’a sai dai don ta zama jangwam, kuma ya rufawa kansa asiri kada bakin duniya ya dame shi. Ita kuwa uwar gidansa (Aina’u) ta daura yakin zama da wannan kishiya har dai a karshe ta gano sirrin da ke dabaibaye da Lubna. Ta bayyana masa cewar lallai Lubna da ciki ta shigo gidannan kuma tana da tabbacin haka.
A daya bangaren na mahaifin Lubna, saboda matsin lamba ya cije ya auri wata matar Hafsa (Rukayya Umar). Tarewarta keda wuya; ba a gama cin amarci ba sai tafiya ta kama mijin inda ya bar dansa domin kula da gida da duk wani sha’ani da matar take bukatar yi. Bayan tafiyarsa ita matar ta bukaci dan mijin nata wato Babangida (Ashiru Nagoma) daya taimaka mata da ci gaban karatunta kada ta rika mantawa. Shi kuma ya yarda da haka. To amma ita da dalilinta ko manufa na wannan bukata. Domin ta fito da maitarta a fili lokacin da ta nemi su yi shedana kuma nan ma shaidan ya samu cin nasara. Tayi amfani da kissa da jan hankali irin wadda take da ita har ya yarda.
Jin dadin da yayi a karonsu na farko shima yaga ya kamata ya ci gaba da darjewarsa. A takaice dai sun sake fadawa cikin wannan aika-aika katsam sai ga mijinta kuma mahaifinsa ya fado dakin ya same su a cikin wannan mummunan hali.

Kashi na Biyu
To sakamakon abinda ya tarar a gidansa tsakanin dansa da amaryarsa nan da nan ya dau matakin korar dan daga gidan. Mahaifinsa ya nemi jin dalilin korar dan da ya haifa daga gidan to amma ya kasa fitowa fili ya bayyana dalilin hakan. To itama dai matar tasa a karakaunar da suka sha ita da dan mijinta, ciki ya samu.
Nasir kuwa ya lura da maganar matarsa inda ya tabbatar da haka a lokacin daya kira Lubna domin jin yadda akayi. Ya bayyana irin soyayyar da yake yi mata amma hakika bashi da wani zabi illa su rabu domin Allah Ya hana auren mace da ciki. To ita dai saboda tsagwaron gaskiyarta ta amsa cewa lallai da ciki ta zo gidan kuma hakika shari’a bata yarda da boye gaskiya ba. Kawai abinda ya dace shine ya dau duk matakin daya yaga dace kamar yadda take gaya masa. To matakin daya dauka shine yi mata saki har uku gaba daya. Amma dai yayi mata nasihar cewar ta lura da duniya, idan kuma da rabon su sake haduwa to shikenan. Suka dai rabu.
Abin boye dai ya fito fili domin maganar cikin da yayi ma ‘yarsa ta fito kowa yasan abin daya wakana. Surukinsa (Kabiru Nakwango) ya zo wurinsa kuma ya fatattake shi da zafafan maganganu kan irin aika-aikar daya aikata. Ya bayyana masa irin zubar da kimarsa da yayi a gaban ‘yarsa da kuma zubar da mutuncin kansa da yayi a idon duniya sakamakon wannan abin tir da yayi. Ya nuna cewar lallai ya zama kwaro, ya zama cinnaka wadda ko a wurin yara sai dai a mitsittsike, ya zama jaba da gizo-gizo kuma ya zama mujiya a cikin tsuntsaye. Mutunci dai ya zube.
Shi kuwa Nasir bayan ya saki Lubna sai Allah Ya hada shi da wata kanwar kawar matarsa lokacin da ta zo domin isar da sako ga matarsa. Ganinsa keda wuya ta fada kogin kaunarsa. Kuma dai a takaice ya aureta duk da matsayin matar tasa bayan yayi mata wayon tura ta kasa mai tsarki kafin ta dawo anyi auren.
Shi kuma Babangida ya bayyana ma kanwarsa dalilansa na aikata aika-aikar da yayi da matar mahaifinsa bayan ita kanwar ta tambayeshi abinda yasa yayi hakan. Ya nuna cewar gaskiya yaji zafin abin da mahaifinsa yayi mata don haka shi yana ganin ya mayar da martani ne kuma ya dauko fansa ne, kuma a ganinsa bai yi wani laifi ba.
Lubna dai saboda zafin abubuwan dake damun ta har kusan ta daina tsoron mahaifinta. Ta fito balo-balo ta gaya masa cewar mijinta ya sake ta kuma ya saurari baragurbin day a fashe a gidansa. Ta bayyana masa cewar kazantar tayi yawa, uba da ‘yarsa.
Gida dai ya zama wani hargitsattse. ‘Ya dauke da cikin da ubanta yayi mata, Mata da cikin da dan mijinta yayi mata. Amma dai ya nemi da matar tasa ta zubar da cikin amma ta tsaya kai da fata cewar lallai sai ta haife. Yadda kowa ya taka kasa haka abinda yake cikinta sai ya taka kasa.
Alhaji kuma ya sake neman wata bazawara (Hajara Usman). To amma zaman bai karko ba saboda samun labarin da tayi na irin abinda ya shafeshi. Ta gaya masa cewar ita tunda take bata taba ganin irin wannan kwado ba; yayiwa ‘yarsa ciki sa’annan dansa yayiwa matarsa cikin. Don haka ta bashi kwanaki uku kan ya sallameta.
A kwana a tashi dai abin boye ya fito fili domin dole aika-aikar ta fito. Lubna da matar mahaifinta sun haihu. Gida ya zama wani iri. Akan tilas Alhaji yake daukar ‘yarsa kuma jika, shi kuma Babangida ya dau dan da matar babansa ta Haifa amma daga gareshi (Babangida).
A karshe dai surikin Alhaji ya tattaro wadanda abin ya shafa wato Alhaji, Lubna, Babangida da Nasir inda ya ragargaji yadda Alhajin ya sha batawa Nasir kan nemen Lubna sai da ta kwabe sa’annan ya lallaba ya bashi ita da aure.
A wannan zama dai an fayyace duk abubuwan da suka faru kuma Alhaji yayi nadamar abinda ya aikata. Don haka surukinsa ya bukace shi da ya nemi gafarar ubangiji da kuma korar gaba bisa sharadin cewar yabi ka’idar tuba wato yin nadama da kuma kudurcewa a zuci ba za’a kara aikatawa ba.
Karshen fim din Fassara kenan.

Sharhi
Hakika wannan fim ya tabo wata babbar matsala kuma annoba da tayi katutu a wadansu gidajen musamman masu kwadayin son abin duniya. Ya nuna irin sakacin wadansu iyayen wajen zama da ‘ya’yansu mata ba tare da wani a tare da su ba. Wannan fim ya nuna shiga hadarin irin wannan zama. Tabbas duk mutumin daya zauna daga shi sai balagaggiyar ‘yarsa to ya shimfidawa shaidan shimfidar zama a gidansa.
Wannan fim ya nuna cewar tabbas, lallai duk abinda mutum ya aikata to ko-bajima-ko-badade sai yaga a kwaryarsa, shima dole ayi masa. Masu hali irin na Alhaji ba zasu ji dadin rayuwarsu ba.
Illar irin wannan hali na kwanciya da ‘ya ko makamancin haka yana da illoli da sakamako da yawa. Ga dai rashin samun sukunin yin aure daga manema, gallazawa daga kishiya ko kawaye, tunanin abinda mutum zai tarar a wurin Ubangijinsa, sa’annan bata zuri’a har abada. Shi kuma mai aikata abin da shi da kwanciyar hankali sun yi sallama. Kullum hankali tashe, hada zuri’a da shi ma jan aiki ne. Kasancewa dan wannan zuri’a ma abin kyama ne kamar yadda Lubna ta yi fatan ina ba a nan gidan Allah Ya halicce ta ba.

Burgewa
Wannan fim babbar fadakarwa ce kuma duk wadanda suke da hannu wajen wannan fim sun cancanci yabo. Kowa yabi irin umarnin da aka bashi musamman Lubna (Hafsa) wacce itace ginshikin duk abinda ya biyo baya. Haka mahaifinta (Shehu Hassan). Allah Ya kara basira amin.
Hakika fim din ya burge. An jawo hankalin masu kallo wajen tsawaita damuwa da Lubna take ciki domin ya kara jan kunne ga mutane masu tunanin aikata irin wannan. Hafsa ta dace da wannan matsayi musamman wajen sanyaya jikin masu kallo.
Yadda Nasir ya nuna tsabagen so gareta amma duk da haka don nunawa jama’a cewar babbar magana ce yasa tilas ya saketa. Matakin daya dauka yana da wuya tunda ya sameta mai kyawun hali. Maganganun da yayi mata lokacin da zai sake ta gaskiya sun ja hankalin mai kallo. Dole ne a jinjina wa mutanen da suke da hannu wajen wannan fim musamman mai bayar da umarni.
Aina’u itama ta nuna irin halin da yawancin matanmu kan nuna musamman idan za ayi musu kishiya. Itama ta burge.
Matsayin Hafsa (Rukayya) ya nuna yadda mata kan yaudari samari domin aikata wata badakala, ta nuna kwarewa wajen hilatarsa domin aikata aikin assha.

'Yan matsaloli
Babban kuskuren wannan fim shine babu wata dangantaka tsakanin rayuwar Mansura da saurayinta da jigon fim din. Ina ganin an dai yi cikon kilo ne don a nishadantar da kuma nuna kwalisa kawai.
Abu na biyu shine kwata-kwata babu muhallin waka da rawa a cikin fim din domin tsabar tausayi da kuma kokarin ganin abinda zai wakana zai sa mai kallo ya tura wakokin fim din gaba.
Lubna tana bayyanawa cewar mahaifinta ya tsare ta har da bindiga idan bata yarda dashi ba, to amma mu mun ga bandaki ya bita har kuma mun ji calla karar da tayi, sai dai watakila ba wannan ne karon farko ba.

No comments: