Sunday, October 12, 2008

SARKI 10 ZAMANI 10

SHARHIN SARKI 10 ZAMANI 10
Yusuf Ubale Ajingi

FIM: Sarki 10 Zamani 10
KAMFANI: Iyke Moore Production
SHIRYAWA: Ibrahim Bauni
LABARI/TSARAWA: Yakubu Muhd
UMARNI: Yakubu Muhd
TAURARI: Ali Nuhu, Sani Musa Danja, T.Y. Shaban, Ubale Ibrahim, Ibrahim Maishunku, Baballe Hayatu, Saratu Gidado, Zainab Mohd, Mansura Isah, Farida Jalal, Hafsatu Sharada da sauransu.


GABATARWA
A wannan zamani na siyasa a Nijeriya akan samu takun saka tsakanin shugabanni da sarakunan gargajiya wajen shugabantar al’umma. Hakan kan sa Sarakunan daurewa ‘nasu’ gindi domin cin zabe ko ta halin kaka. Har ila yau tserereniyar neman mulki takan jawo rufewar idon hatta ‘yan uwa musamman masu jinin sarauta, idonsu kan rufe su shiga matsananciyar gaba. Hakan ya kan ci gaba har zuri’a mai tsaho. Wannan ya kan zama su kansu mutane sun rasa madafa tattare masu shugabantarsu wadda tsananin son shugabancin kan saka idon shugabanni ya rufe su manta da talakawansu sai dai tunanin yadda zasu dauwama a mulki ko kece raini. Kuma koda wata badakala ta bullo musu ba zasu ba da kai bori ya hau ba, a’a sai su biya wadansu masu baki su fita gidajen rediyo suyi ta surutun kare shugabannin ko da basu da gaskiya. Wannan har ya zama yadda mulki gargajiya yake shima na zamanin (siyasa) ya ke nema ya zama.

LABARI
Labarin wani gidan sarauta ne inda bayan rasuwar Sarki, aka samu rabuwar kai wajen nada sabon Sarki wanda a bisa al’ada ya kamata a ce babban dan ne zai gaje shi. To amma kamar yadda ya zama ruwan dare a wannan zamani rigima ta kaure tsakanin mahaifiyar babban dan sarki (Ali Nuhu) wato Saratu Gidado da mahaifiyar kaninsa (Sani Danja) wato Zainab Mohd. To amma dai an dage da kasancewar babban dan ya zama Sarki. To amma ita mahaifiyarsa ta ci gaba da nuna kiyayyarta ga Sarautar Sarki Ali ta kuma ci gaba da haddasa kiyayya a tsakaninsu. Ana haka har dabara tazo mata ta baiwa danta shawarar ya fito takarar gwamnan jihar.

Labari ya iske Sarki inda shi kuma domin tsira da kujerarsa ya sanya kaninsa (Ubale Ibrahim) ya fito shima a matsayin dan takarar gwamna. To an dai yi zabe kuma Sani Musa shi jama’a suka zaba.

Duk da kin yin mubaya’a da sarki yaki yi ga sabon gwamna bai sa ya nemi daukar wani mataki ba har sai lokacin da mahaifiyarsa ta tilasta masa kan dole ya tsige Sarki. Hakan kuwa a kayi. Kwatsam gwamna ya kori Sarki ya kuma nada dan uwansa (Ibrahim Maishinku) a matsayin sabon sarki.

Wannan abu ya yiwa bangaren tsohon sarki ciwo inda daya daga cikin ‘ya’yansa mata wacce ta kasance fandararriya (Farida Jalal) ta ci alwashin daukar fansa. Tun da daman babban dan gwamna Dini (T.Y. Shaban) wanda shima manemin mata ne kuma mai kafafa da mulkin ubansa ya nemi ita ‘yar Sarki amma taki, to sai dabara ta fado mata inda ta taka har gida ta sameshi kan cewar tana sonsa. Duk da kin yardar mahaifiyarsa (Mansura Isah) amma ya ci gaba da zuwa wurinta tare da daukarta su zagaya wurare.

Ana cikin haka kwatsam sai ta bayyana masa cewar ta samu juna biyu da shi. Abin ya dame shi. Kakarsa ta nemi a zubar da cikin domin abinda ke gabansu shine zarcewa ko mikewa da mulki amma yarinyar ta kekasa kasa tace ita kam ba zata zubar ba, kuma wannan shine daukar fansar da ta yi alkawari zata yi. Saboda tsananin kwadayin dauwama a mulki kakar ta zuga shi kan ya aika da yarinyar barzahu. Ai kuwa hakan akayi. A lokacin kisan, abokinsa Umar (Adam A. Zango) ya nuna rashin dacewar aikata hakan to amma ba makawa sai da suka kashe ta.

Anyi kullin yadda za’a juya kisan kan Umar saboda furucin da yayi na kin rufe bakinsa amma dalilin kulli kurciya da ya rika yi da jami’an tsaro karkashin Inspector (Bash Qaya) a karshe dai Umar ya gayyaci ‘yan jarida domi bayyana musu labari mai ban mamaki. Ya bayyana labarin nasa ne a lokacin da ya rutsa Dan gwamna har ya harbe shi a kafa. Tilas dan gwamna ya bayyana gaskiyar lamari. Wannan labari shi ya yi tasirin faduwar gwamna a zaben neman zarcewa kuma kanin tubabben Sarki wato Ubale Ibrahim shi ya ci mukamin na gwamna. Shi kuma yaci alwashin rama cin mutuncin da akayi musu.

SHARHI
Labarin ya fito a lokacin da tsananin neman mulki da kuma dawwama akai ya zama ruwan dare. Ya kuma fito lokacin da masu mulkin gargajiya ke shiga cikin harkokin siyasa wanda kan jawo faduwar darajarsu. Fim din ya nuna yadda rigima kan kaure tsakanin ‘ya’yan sarakuna hart a ci gaba zuwa jikoki.

Wani abin burgewa shine kokarin nuna al’adar gidan Sarauta. Har ila yau ba’a wakoki ba illa guda daya wadda ita ma ta burge domin kalaman gasa da ‘ya’yan gwamna dana Sarki. Kida-kiden da aka rinka saka wa sun dace da na gargajiya. Su ma ‘yan wasa sun burge kuma sun yi biyayya ga darakta musamman mahaifiyar gwamna, da ‘yar Sarki.

DARUSSA
Fim din ya fito da:
* Yadda gaba ke ruruwa tsakanin ‘yan uwa saboda sarauta musamman idan magabta sun shiga tsakani.
* Yadda mutane da a wannan zamani kan shiga harkokin siyasa domin daukar fansa.
* Yadda ‘ya’yan masu mulki kan janyowa iyayensu abin fadi.
* Yadda hakurin yak e kasancewa maganin zaman duniya.
* Yadda gaskiya take yin halinta komai tsanani da tsawon zamani.
* Nuna idan mai mulki yana son dauwama a mulki to dole ya kula da tarbiyyar ‘ya’yansa.
* Nuna yadda maganar iyaye mata kan yi tasiri a zukatan ‘ya’yansu. Idan suna fadar alheri su ga alheri idan tsiya to su ga tsiya.

MATSALOLI
Duk da kasancewar labarin yana da karfi to amma akwai ‘yan matsaloli ko gyare-gyare daya kamata a ce masu fim din sun lura da su kuma watakila zasu fito a kashi na biyun fim din.
* Saboda son tarbiyantar da ‘ya’yansa bai kamata ace ‘yar sarki tayi amfani da zina wajen neman mafita ba.
* Bai kamata shi kansa sarki ya dogara da ‘yarsa ba wajen daukar fansa domin ta yaro kyau take amma ba ta karko.
* Ba ‘a nuna matsayin adalcin Sarki ba ta yadda watakila tsige shi zai iya janyo tarzoma ko makamancin haka ba. Haka shima gwamna kila adalci ko rashinsa zai iya saka jama’a su goyi bayansa.
* Mun ga fadawan Sarki da rawani da sauran shiga ta mulkin gargajiyar Hausawa amma abin mamaki ban ga Sarki da rawani ba sai dai alkyabba da kuma hula da ake dora musu maimakon nadin rawani. Shin ko wanne bangaren kasar Hausa a ke nufi a wannan fim domin wata kila masu bincike a wasu kasashe zasu kasa gane yadda yanayin shigar Sarki da suke karantawa da wacce fim din zai nuna musu.
* Bayan tsige Sarki ba’a nuna shi yana wani kokari ba sai aka bar abin a hannun yara. Shin me Sarki ke ciki?
* Shin tubabben Sarki ya halasta cikin da ‘yarsa tayi ne bai dau wani mataki ba?
* Me yasa tsigaggen Sarkin bai dauki wani mataki na bin hakkin ran ‘yarsa ba, kawai sai dai gwamna shi kadai don shima ya tsira da kujerarsa?
* Shin tsige Sarki yana da sauki a wajen mutum daya misali yadda gwamna ya yanke hukumci?
* Shin dole ne yin ciki ne kawai zai iya girgiza kujerar masu mulki? Me ya sa babu wata badakala da za’a kirkira a madadin hakan?
* Shin daukar aikata fasadi a matsayin hanyar daukar fansa ba zai zamo abin koyo ga ‘ya’yan da iyayensu suka rasa kujerarsu ba?
* Shin yawan tsige Sarakuna da aka nuna ba zai zamo kamar wasan yara ba musamman a idon sauran al’umma ba?
* Shin me yasa gwamna bashi da mashawarta sai mata?
* Me ya sa aka sakawa fim din suna Sarki 10 zamani 10? Ina ga kamar yana nuna idan ka na mulki to ka aikata abinda kaga dama domin lokacinka ne.
* Ya kamata a ce sabon gwamna ya yi kokarin kawo adalci maimakon shima ya ci alwashi daukar fansa. Hakan zai sa har abada mulki ya lalace.
* Ya kamata a ce addu’ar da Waziri yayi (Isah Bello) bayan idar da Sallah ta neman samun gwamna mai adalci ta yi tasiri sabanin alamun yadda sabon gwamna ya nuna.
* A bangon gidan fim din an rubuta Iyke Moore Production, a cikin fim din an rubuta Al’umma Production ke gabatar da fim din.

KAREWA
Ban taba ganin wani ya fito ko masu fim ko daraktoci ya kare ko bayani kan gyare-gyaren da masu sharhi su ke yi ba. Ya kamata idan har an yi amfani da wani gyara to masu fim su fito su bayyana domin masu sharhin su gane ba aikin banza suke ba. Kuma ina jaddada musu cewar su masu manazartan/masharhanta ba wai wasu kwararraru ne da suka fi masu yin fim kwakwalwa ba a’a suna dai fadar albarkacin bakinsu ne da kuma yadda suke ‘tunanin’ jama’a ke kallon finafinan.

Yana kuma da kyau ko da ba’a amfani da ‘consultants’ a wajen yin fim din to ya kamata a rinka dan raba finafinan ga jama’ar da ke kusa da wadanda suka yi domin samun gyara ko Karin shawarwari.