Tuesday, February 8, 2011

SIYASA!!!

A gaskiya a fahimtar da nake da ita kamar har yanzu 'yan siyasa ba su da niyyar gyara al'amuransu. A takaice burin 'yan siyasar Nijeriya shine su shiga a dama da su ko ta halin k'ak'a, wannan shine ummul haba'isin na shiga da fita daga wannan jam'iyyar siyasa zuwa waccan, musamman idan an hana su takara a jam'iyyarsu. Bana son kiran suna, amma duk yawancin wadanda suka fita daga wasu jam'iyyu zuwa CPC wacce Janar mai ritaya Muhammadu Buhari ya assasa to masu kwadayin mulki ne tare da yin amfani da sunan Janar din domin cimma burinsu. Wannan ne ma dalilin da ya sa na sha yin muhawara da mutane cewar ni ban ga bambanci a jam'iyyun Nijeriya ba. ANPP, PDP, CPC, ACPN, ACN, dss suna ne kawai ya bambanta su amma a irin mutanen da suka cika jam'iyyun ba bambanci. Salon mulkinsu daya sai dai idan dama bata samu ba.
Wasu abubuwan ban haushi da ke dabaibaye jam'iyyun sune munafurci, rashin gaskiya, karya, karya alkawari, babakere, yaudara dss. Wadannan da wasu sune shika-shikan siyasar Nijeriya. Menene cin ribar karya, yaudara da sauransu a wajen cim ma buri.
Na samu kaina cikin harkokin siyasa a watannin baya ba tare da ina so ba; domin tun fil azal bana kaunar siyasa saboda yarda da nayi cewar babu ingantacciyar hanya ta mulki illa wacce Allah subhanahu wa ta'ala ya shimfida. Dun wata hanya da ta kaucewa abinda Ya ce mu bi to lallai ba inda zata kaimu sai rami (wagegen ramin da ba zamu iya fitowa ba). Ni ba malami bane, amma bisa dan zaman da nayi a jami'a sau biyu da dan sauraron karatu da nake a duk inda na samu kaina ya sa na tsani harkokin siyasa. A wacce hujja zan bi abinda na fahimta karya ce.
Na samu kaina cikin rudani da tunani tun farar ta fari bana ganin siyasa da darajar kwayar zarra, don haka zuciyata ta ki yarda da bin son rai na. An kasa samun daidaito tsakanin son na cikawa wani burinsa ko wani gungu na jama'a da hakikanin cikin zuciyata. Wallahi ko da na daure kan son ra'ayin wani dan siyasa sai na kasa domin duk inda kake bukatar son abinda baka so to akwai wahala. Sau da yawa na kan ga mutane suna rubibin son wani dan takara ko shugaba, amma ko da na dage kan na so shi ba zan iya ba domin tubalin da aka dora shi a kai yana da tsaguwa wacce zata iya rusa ginin da yake kai.
Na lura son kai yayi dan siyasa yawa, koda a siyasance ba daidai ba ne amma shi sai ya kafe kan haka. An dora min mukamin da na rike ne ba domin ina da kishin jama'a ba, an bani ba don ana sona na rike mukamin ba a'a sai domin a yi amfani da sunana don samun abinda ake bukata, an bani domin na samu inda zan rika kashe dan abinda nake samu.
Na yi dana-sanin dan rikon da nayi domin na yi mamakin ga mutane masu kaunar mukamin amma an hana su, na kallaci irina masu son ganin ci gaba da amfani da karatun da suka yi wajen aiwatar da wasu abubuwa a al'umma amma an dora min nauyin da zai hana ni.
Na yi mamakin me yasa ba zasu dauko wasu ba sai ni? Wani abin mamakin shine kowa hankalinsa kwance, idan ya taso daga aiki sai ya tafi wurin iyalinsa ya huta amma ni da na dawo gida to sallama za'ayi min. Bani da 'yancin ziyartar wanda na ga dama. Wani abin mamaki shine abokai da muka taso tare, 'yan ajinmu da wadanda mu ka yi makaranta tare an raba mu; duk lokacin da aka ganmu tare musamman idan suna da ra'ayin siyasa da ban to zagi zan yi ta sha. Kai Allah Ya kiyashe mu da irin wannan ra'ayi na siyasa.
Duk abinda nake yi wadda na saba a baya, yanzu ba don Allah nake yi ba, sai domin ina neman mukami.

A rubutu na gaba zan kawo wasu maganganu na addini da na kallata da suka sanya na yi bara'a da harkokin siyasar Nijeriya.

No comments: