Monday, August 11, 2008

NEMAN GYARAN HALAYYAR ‘YAN FIM


A kwana a tashi yau gashi an shafe shekara guda da faruwar badakalar Maryam Usman. Allah cikin ikonSa har kuma an samu karuwa. Kowa ya sha fadin ra'ayinsa kan abinda ya faru da kuma hanyoyin da ake ganin zasu kawo gyara. To ni ma a wancan lokaci na fadi ra'ayoyina. Wannan da ke kasa daya ne daga cikinsu domin tunawa da baya wanda Bahaushe ke cewa shine roko.
Ko da yake abinda zai faru ya riga ya faru. Wannan Magana ta dade tana yawo a tsakanin ‘yan industri ta finafinan Hausa. Farkon abin a matsayin jita-jita yake yawo wadda har aka samu watanni. A hankali abin yana yawo har sai yanzu ya bayyana karara. To a gaskiya an fadi ra’ayoyi iri-iri kuma har yanzu wadannan ra’ayoyi basu kare ba. Abinda aka sani dai duk abin ya riga ya faru sai dai neman gyara a gaba. Amma abin bakin ciki ne kuma abin tausayi wanda bai taba faruwa a masana’antar finafinan Hausa ba.
To amma duk da haka fadar ra’ayi ya zama dole. Tun kafin wannan badakala ta wakana ake ta yin korafi game da halayyar ‘yan fim musamman mata. Ta kowanne bangare kalubale ne gasu ‘yan fim to amma matsayinsu shine su dai fadakarwa suke. Sun tsaya akan lallai su masu fadakarwa ne kuma ma ai akwai wadanda suka fi su iskanci a gari suna yawo amma ba wanda yace musu kanzil. Don me su za’a damesu. To an sha samun ra’ayuyyuka kan wannan. Ni ina ganin duk mutumin da yace shi malami ne mai koyar da dalibai ko almajirai ko sauran jama’a to yana tare da sa-ido. Da zarar ya aikata ba daidai ba to jama’a zasu yi masa caa domin shi ya kamata ya nuna yadda ya kamata ayi tarbiyya. Amma wanda halayyarsa dama a fandare take ya zama tantiri to lallai a gari ba a cika damuwa da duk wani iskanci da yayi ba. Ba kuma labari bane a wurin jama’a don yayi hakan.
A rayuwar mu ta yau da kullum kowa ya san irin fasikancin da ake yi. Idan mutum bai gani da idonsa ba to zai ji labari. Kuma muna munafurtar kamu ne domin a wadansu lokutan masu yawan surutun suna wannan aika-aikar to amma bambancin abinda ya faru yanzu shine ya shafi irin wadanda suke cewar su fadakarwa suke kuma an fito da wani tsari na daukar abin a bidiyance a ka kuma yada shi a duniya kowa ya gani. Wannan shine bambancin wannan matsala da abinda yake faruwa. Wadansu wadanda suke farwa Hiyana suma suna da nasu abin asshan ko dai a ciki ko wajen wannan harka.
An sha tattaunawa kuma na taba fada a majalisar finanafin Hausa ta intanet cewar bazan yi mamakin duk abinda ‘yan fim suka aikata ba domin suna yi kuma an sani. Matsalar shine an ki shawo kan abin. Laifin jama’a masu kallonsu ne ko gwamnati ko kuma shugabannin su masu fadakarwar ne. Kai na tabbata akwai abubuwa da aka sha aikatawa wanda ko kare ba zai ci ba amma an ki yin wani abu. Kuma yadda abubuwa suke wucewa sasakai to na tabbata duk hayaniyar da ake yi yanzu idan ba’ayi hankali ba a banza zata wuce kuma zamu gani. Idan kuma ana son ganin rashin faruwar makamancin wannan to mun zubawa shugabannin ‘yan wasan da kuma gwamnati ido.
Shawarwarin da nake dasu kan matakan daya kamata a dauka sun hada da:
Tantance halascin shigowar ‘yan wasa. Misali, kawai sai kaji yarinya tace wai da yardar iyayenta ta shigo bayan karya ce zalla. Idan ma da izinin to zaka tarar mahaifiyarta ce ta amince babu sanin mahaifin domin tare suke da mahaifiyar kila sun rabu da mahaifin na ta ko kuma ya rasu. Ita kuwa saboda rauni irin nasu na son kawa da kyale-kyale sai su kyalesu. Kuma wata da aurenta zata zo amma ba wanda zai bincika sai dai idan mijinta ya zo a yi ta rigima.
Tantace halayyar ‘yan wasa. Mal. Jibrin Fagge ya bayar da misalin zuwan wata daga Nijar ana cikin wannan badakala wai tazo shiga fim. Kawai sai mutum tsilif ya tsallako sakaka yace wai a saka shi a fim. Da wacce manufa ya shigo? Oho! Sai kawai a jefa shi ciki sai kuma wata tsiya ta faru a rasa yadda za’ayi. Ya kamata a je a zauna da iyayensu tare da kafa musu hujjoji kafin a yarda da shigowarsu. Wannan zai sa su su san cewar ba fa kara-zube suke ba.
Ya kamata gwamnati ta tabbatar da rajistar da kungiyoyin masu wasan fim domin lura da irin halayyarsu yadda da matsala ta samu za’a dakatar ko korar dan wasa.
Ya kamata a samu kamfanoni domin zabo ‘yan wasa. Hakan zai kara nuna amfanin rajistar ‘yan wasan da kuma kara daukar kansu a masayin wani jinsin mutane mai amfani da muhimmanci a cikin al’umma.
‘Yan jaridu su dage wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin bin tsarin addini da al’ada a cikin finafinan mu.
Domin tabbatar da da’a ya kamata a duba dukkan bangarorin yin fim misali yadda a ke wakokin cikin finafinan.
Jama’a masu kallo su rinka takawa duk wani fim da bai dace ba burki musamman a gidajensu. Su kuma rika fadawa mutane ta yadda hakan zai rage kasuwar shi wannan fim.
Ina fatan Allah Ya kare faruwar makamancin wannan abu, Allah Ya tsarkake dukkan ‘yan wasanmu domin samun fadakarwa wacce ta kamacemu da kuma daukakar wannan industri nake kuma fatan za’a gafartawa juna da nemawa wadanda suka yi wannan abu addu’ar neman gafara da shiriya.

No comments: